Gwamnatin Tarayya ta janye ƙarar da ta shigar akan Sanata Natasha

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ce ta janye ƙarar da ta shigar akan Sanatar mazaɓar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Natasha Akpoti-Uduaghan, wadda ke tuhumar ta da laifin ɓatanci.

A cewar takardar janye ƙarar da aka gabatar a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja da aka fitar a ranar Lahadi mai lamba FHC/ABJ/CR/195/2025, Ofishin Antoni Janar na Ƙasa (AGF) ne ya nemi a dakatar da cigaba da shari’ar.

Takardar, wadda aka sanya wa hannu a ranar 12 ga Disamba 2025, ta nuna cewa an ɗauki matakin ne bisa tanade-tanaden sashe na 108(1), 108(2)(a), da 108(5) na na manyan laifuka na shekarar 2015.

A saƙon janye ƙarar, ofishin AGF na ya ce: “Ofishin Anton Janar na ƙasa ya bayyana cewa, yana son janye cigaba da shari’a akan wannan batu.”

Saidai har zuwa yanzu ba a bayyana dalilan janye ƙarar ba, amma matakin ya nuna kawo ƙarshen jerin tuhume-tuhumen da ake yi wa sanatar tun lokacin da aka shigar da ƙara ta kotu.

Kazalika, har yanzu babu wata sanarwa daga ɓangaren sanatar game da matakin, yayin da ake sa ran kotu za ta jingine shari’ar bayan janyewar gwamnati.

An tuhume ta da zargin ɓatanci ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello cewa suna kitsa yadda za a halaka ta.

By ukarofi