Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rahotanni daga ƙasar Ingila sun tabbatar da cewa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta kori mai horar da ‘yan wasanta, Ruben Amorim bayan shafe watanni 14 a matsayin.
TheAlthletic ta wallafa haka ta kafar X a safiyar yau Litinin, inda ta ƙara da cewa, mataimaki Darren Fletcher ne zai maye gurbinsa na wucin-gadi.
Sanarwar ta bayyana cewa, tuni aka sanar da kocin mai shekaru 40 kuma ɗan ƙasar Portugal matakin a hukumance.
Ana ganin hakan na da alaƙa da rashin nasara akai-akai da ƙungiyar ta ke yi musamman a gasar Premier League ta ƙasar.
Sauran bayanai za su biyo
