Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A jiya Lahadi aka gudanar da jana’izar abokan tsohon
zakaran damben nan, Anthony Joshua da hatsari ya yi sanadiyyar rasuwarsu a babbar hanyar Legas a ranar Litinin ɗin da ta gabata.
Idan za a tuna, hatsarin ya rutsa da Joshua ne, wanda ya jikkata da kuma Sina Ghami da Abdul Latif Kevin Ayodele da suka rasu.
An ga yadda mutane da dama suka taru a Babban Masallacin Birnin Landon domin yi wa mamatan jana’iza, inda kuma aka binne su a maƙabartar Hendon.
Iftila’in ya same su ne a lokacin da suka zo Nijeriya hutu, sakamakon cin karo da wata tirela maƙare da kaya ta abin da Hukumar Kiyaye Haɗurra (FRSC) ta kira da gudu sama da kima.
Daga bisani hukumar ‘yan sanda a Jihar Ogun ta kama direban motar, wato Adeniyi Mobolaji Kayode tare da gurfanar da shi a gaban kotu domin yin bayanin haƙiƙanin abin da ya sababba hatsarin.
Bayan haka ne aka bada belinsa akan Naira miliyan biyar, sannan kuma aka tsare shi har zuwa lokacin da zai cika sharuɗɗan belin.
An haifi Joshua, mai shekaru 36 ne a Watford na ƙasar Ingila ta iyaye ‘yan Nijeriya, wanda ya zo hutu Nijeriya tare da abokansa bayan nasarar Jake Paul da ya samu a Miami a ranar 19 ga watan Disamba, 2025.
