Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shehun Malami Muhammad Rabi’u Dan Tinki, wanda ake kira da Malam Rabi’u ɗan Yunusa ɗan Alhasan ɗan Baru, ya kasance ɗaya daga cikin manyan fitattun malamai da suka bar gagarumin tarihi a fagen ilimin Alƙur’ani da karatun addini a Arewacin Nijeriya.
An haife shi a shekarar 1897 a garin Tinki, da ke ƙaramar Hukumar Bichi a Jihar Kano, a cikin gida mai tushe na ilimi da addini.
Tun yana ƙarami, Malam Rabi’u ya taso cikin tarbiyya da ladabi, duk da kasancewarsa mai son wasannin yara da mu’amala da takwarorinsa. Mahaifinsa shi ne malaminsa na farko, inda ya soma koyon Alƙur’ani da harsashen ilimin addini tun yana ƙuruciya. Saboda hazaƙarsa da jajircewarsa, ya haddace Alƙur’ani gaba ɗaya tun yana da kimanin shekara goma sha huɗu, abin da ya nuna irin basirar da Allah Ya hore masa tun a fari.
Bayan kammala haddar Alƙur’ani, Malam Rabi’u ya zurfafa cikin karatun littatafan ilimi, inda ya fara da muhimman littattafai kamar Ahalari da Iziyya, yana ƙara gina tubalin iliminsa a nahawu da ilimin harshe. Daga nan, sha’awarsa ga neman ilimi ta sa ya nemi izinin mahaifinsa domin bin manyan malamai a waje.
A wannan tafiya ta neman ilimi, ya fara da zuwa wajen shahararren malami Malam Kunta, inda ya zauna tsawon lokaci yana ɗaukar ilimi da tarbiyya. Bayan haka, sai ya nufi Damagaram a Jamhuriyar Nijar, inda ya zauna a gaban Mahiru Kalla, ɗaya daga cikin fitattun malaman ƙira’a a zamaninsa. A wurinsa, Malam Rabi’u ya shafe lokaci mai tsawo yana sauke manyan littattafai a fannoni daban-daban na ilimin ƙira’a da Tauhid. Daga cikin littattafan da ya karanta akwai Nuniyyar Sakaawiy, Hidayatussibiyan, Tuhfatul Adfal, Muƙaddimat Jazary, Shaɗibiyya da Lamiyyatul ƙira’at, wazanda suka ƙarfafa shi sosai a ilimin karatun Alƙur’ani da hanyoyinsa.
Ba tare da gajiya ba, Shehun malamin ya ci gaba da yawon neman ilimi, inda ya dangana zuwa Maiduguri domin yin karatu a wurin Mahiru Ahmad. Wannan tafiya ta ƙƙra masa faɗin sani da gogayya da malamai daga sassa daban-daban na yankin. Daga Maiduguri, ya dawo Kano, ya sauka Haɗeja, inda ya ƙara duƙuta da zurfafa ilimi a gaban Malam Is’hak, kafin daga bisani ya koma Kano ya fara koyarwa da faɗaɗa ilimi ga jama’a.
Lokacin da labarin shahararren malami Mahiru Hamid ya kai kunnen Malam Rabi’u, sai zuciyarsa ta ƙara motsuwa, ya nemi izinin zama almajirinsa. A nan ne ya ƙara zurfafa a fannin dabti, wanda shi ma muhimmin ɓangare ne na ilimin Rasmu da wasullan Alƙur’ani. Wannan fanni ya sanya shi ya zama ɗaya daga cikin malamai masu ƙwarewa sosai a tsare-tsaren rubutun Alƙur’ani da ƙa’idojinsa.
A lokacin karatunsa a wurin Gwani Hamid, Malam Rabi’u ya yi karatu tare da manyan malamai da dama, waɗanda daga bisani suka zama fitattun masana a kansu. Daga cikinsu akwai Malam ɗan Gunduwawa, Malam Aliyu Mai Kwaro, Malam ɗan Karofin Yashi, Malam Yunus ɗan Gumel, Malam ɗan Kanuri, Malam Isah ɗan Kwandarai, Malam Sabo ƙofar Wambai da Malam Umar ɗan Mai-Rigar-Fatu. Wannan muhalli ya kasance makaranta ta musamman wadda ta samar da manyan malamai masu tasiri a al’umma.
Shehun Malami Muhammad Rabi’u ɗan Tinki ya shahara da halaye na kawaici, haƙuri, sauƙin kai da kusanci da jama’a. Iliminsa bai taƙaitu a littattafai kaɗai ba, har ya haɗu da kyakkyawar tarbiyya da aiki da ilimi a aikace. Bayan rasuwarsa a shekarar 1959, tasirin iliminsa bai gushe ba, domin tsangayarsa ta ci gaba da bunƙasa, ta samar da rassa da dama a faɗin yankuna.
Wannan tsangaya tana ci gaba da rayuwa a hannun ɗansa, Halifa marigayi Sheikh Is’haka Rabi’u, wanda ya gaji tutar ilimi da hidimar Alƙur’ani da addini, ya ci gaba da riƙe gadon da mahaifinsa ya bari kafin Allah Ya yi masa rasuwa a shekarar 2018. Tarihin Malam Rabi’u ɗan Tinki ya kasance shaida cewa ilimi, jajircewa da tsantsar niyya suna iya barin abin tunawa da ba ya gushewa a zukatan al’umma.
