Zubar gashi: Dalilai da illoli da matakan kariya

Spread the love

Gabatarwa:

Mata da dama suna shiga wani yanayi marar daɗi kan yadda gashinsu yake zubewa. A duk lokacin da suke yin ƙorafi sukan ce “gashinsu yana zuba ba gaira babu dalili”Gashi ya kasance wani muhimmin ɓangare ne na kamannin mutum, musamman ma ga mata. A yawancin al’adu, ana kallon gashi a matsayin kwalliya, ɗaukaka, ko kuma ƙyau. Saboda haka, zubar gashi (wanda ake kira alopecia a harshen kimiyya) na iya shafar mutum ta fuskar damuwa da kuma rashin walwalar rayuwa.

A wannan rubutu, za mu duba me ke janyo zubar gashi, nau’o’in zubar gashi, hanyoyin rigakafi da kuma matakan da za a ɗauka don magance shi.

Ma’anar Zubar Gashi (Hair Loss)

Zubar gashi yana faruwa ne lokacin da yawan gashin da ke zubewa ya fi yawan gashin da ke tasowa. Da al’ada, mutum na iya rasa kimanin 50 zuwa 100 a rana. Amma idan gashi ya fara zubewa fiye da haka, yana iya zama matsala ta lafiya.

Nau’o’in zubar gashi:

1 Zubar gashi na gado (genetics):

Idan iyayen mutum ko danginsa suna fama da zubar gashi, to yana da yuwuwar hakan ya shafe shi.

Ana kiransa male pattern baldness ko female pattern hair loss.

Wato dai gado ne daga iyaye zuwa ‘ya’ya.

Yana tasowa a hankali, musamman daga saman kai ko goshi.

2. Canjin wasu ƙwayoyin halitta  (hormone):

A lokacin ciki da haihuwa da shayarwa da lokacin da mata suka kai wani mataki na Menopause Ko cututtuka masu nasaba da hormone kamar Polycystic Ovary Syndrome (PCOS)

3. Zubar gashi  a wasu ɓangarori na kai (patches):

Yana da nasaba da autoimmune disease wato raunin garkuwar jikin mutum wadda wannan raunin yana yana iya shafar gashi.

4. Nau’in zubar gashi na wucingadi 

Akwai wasu nau’ukan zubar gashi wanda wasu dalilai kan kawo su kuma in wannan dalilin ya kau sai zubar gashin ta dakata. Misali ,bayan damuwa mai tsanani a jiki ko  rashin abinci ko  ciwo ko tiyata. Gashi yakan zube da yawa lokaci guda.

5. Zubar gashi ta ƙarfi (traction alopecia):

Wannan nau’in zubar gashin yana faruwa ne sakamakon jan gashi sosai ko kitso mai tsauri.

6. Ciwon da ke lalata gashin kai:

Akwai nau’ukan ciwo wanda kai tsaye suke shafar kai ko kuma nau’in magungunansu suke shafar gashi kai tsaye. Duka waɗannan nau’oin zubar gashi ana buƙatar kulawa ta musamman don magance matsalar, kuma in an samu ahalin abin ana dacewa da waraka. 

7. Rashin abinci mai gina jiki:

Iya matsalar rashin abinci mai gina jiki na janyo zubar gashi. Misali iron (karfe), zinc, biotin (Vitamin B7), protein, da Vitamin D na iya janyo gashi ya zube.

8. Damuwa da gajiya  (stress):

Damuwa mai tsanani na jiki ko na tunani na iya hana gashi girma kuma ya sa ya zube. Sau da dama mata da suke fama da wannan matsalar damuwa ita ce ke janyowa.

9. Ciwon fatar kai  (scalp infections):

Fatar kai kamar sauran fata ta jikin ɗan’adam tana iya haɗuwa da larura wadda takan iya haifar da zubar gashi.Akwai kwayoyin cuta  da ke ɗauke da fungal infection (kamar tinea capitis) ko bacterial infection.

10. Magunguna:

Magungunan cutar cancer (chemotherapy) da hawan jini da  ciwon sukari da cutocin damuwa da ma wasu na tazarar iyali akan samu waɗanda suke haifar da zubar gashi. (amma masana kiwon lafiya su suka san waɗanne ne kuma aikinsu ya fi zubar lafiyar muhimmanci)

11. Yin wankin gashi ko tsari mai tsauri:

Yawan amfani da sinadarai masu ƙarfi, wanke gashi da ruwa mai zafi, ko amfani da kayan gyara gashi masu cutarwa ko na bogi ko kuma waɗanda wa’adin aikinsu ya ƙare ko wajen wanke kai wanda ba shi da inganci ko ƙarancin kwarewa duka suna haifar da zubar gashi.

12. Cutar ‘Autoimmune’:

Jikin mutum yana kai hari gashin kansa kamar a alopecia areata.

13. Zazzabi mai tsanani ko tiyata:

Bayan jinya ko cuta mai tsanani, gashi yakan shiga “resting phase” kuma ya zube bayan watanni 2–3.

14. Tsufa:

Yau da gobe sai Allah. Yawan shekaru da yawaitar furfura da gajiyawa wurin kula da gyara na kai duka suna haifar da zubar gashi.

Zan ci gaba a mako mai zuwa insha Allahu.

By ukarofi