Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Haka kuma hukumar ta kama ƙwayoyi masu nauyin Kilo 2,400 a shekarar 2025.
Kwamandan hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) a Jihar Katsina CN Sama’ila Danmalam ya bayyana haka a hira da manema labarai.
Ya ce hukumar ta samu gagarumar nasara a yaƙin da take yi da shan miyagun ƙwayoyi da safararsu a shekarar 2025, inda ta kama mutum 1,018 tare da ƙwace miyagun ƙwayoyi masu nauyin sama da kilo 2,400.
A cewarsa, nasarorin da aka samu sun biyo bayan dabarun aiki da jami’an hukumar a Katsina ke amfani da su a ƙarƙashin jagorancin shugaban hukumar na ƙasa, Birgediya Janar Muhammed Buba Marwa (Rtd), na daƙile hanyoyin samar da miyagun ƙwayoyi da kuma rage yaɗuwar su a tsakanin al’umma.
Danmalam ya ce, “a shekarar 2025, jami’an NDLEA sun gudanar da samame bisa sahihan bayanan sirri da sintiri a sassa daban-daban na jihar, lamarin da ya haifar da tarwatsa hanyoyin safarar miyagun ƙwayoyi.”ya ce.
” Mutanen da aka kama sun haɗa da maza 992 sai mata kuma 26.” In ji Danmalam.
Ya ci gaba da cewar, “NDLEA ta samu nasarar kwace nauo’in ƙwayoyi daban-daban da suka haɗa da: Cannabis kilo 1,667.747, Codeine kilo 12.348, da kuma psychotropic kilo 793.66, wanda ya kai jimillar kilo 2,473.755,”kwamandan ya ce.
Harwayau, kwamandan ya kuma bayyana cewar shirin farmaki na mai taken “War Against Drug Abuse (WADA)” ya taka muhimmiyar rawa wajen rage shan miyagun ƙwayoyi a jihar; “an gudanar da shirye-shiryen wayar da kai guda 203, inda mutane 75,135 suka amfana. Haka kuma, an ba mutane 451 shawarwari na musamman, yayin da aka shigar da mutane 58 cibiyoyin gyaran hali na masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.” In ji shi
Ya bayyana cewa, a ɓangaren shari’a, hukumar ta gurfanar da mutane 86 a gaban kotu, yayin da aka samu hukunce-hukuncen shari’a har guda 87 a kan masu laifi.
Danmalam ya koka tare da bayyana irin ƙalubalen da hukumar ke fuskanta, na kayan aiki, musamman ƙarancin motocin aiki, ƙarancin ofis da masaukin jami’ai a faɗin jihar a matsayin abin da ke ci masu tuwo a ƙwarya.
CN Danmalam na kira ga gwamnati jihar Katsina da sauran masu ruwa da tsaki da su bada gudummawa domin shawo kan matsalolin.
Ya jinjina ga Shugaban hukumar NDLEA na ƙasa, Birgediya Janar Muhammed Buba Marwa (Rtd), bisa irin sauye-sauyen da ya kawo a hukumar, tare da taya shi murnar sake naɗa shi da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi.
Haka kuma, ya yi godiya da yaba wa Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umaru Raɗɗa bisa tallafin da take bai wa hukumar, musamman na gyaran motocin aiki da ɗaukar nauyin shirye-shiryen gyara halayen masu ta’ammuli da shan ƙwayoyi.
Kwamandan ya kuma yabawa sarakunan Katsina da Daura bisa shawarwari da haɗin gwiwar da suke yi da hukumar.
Ya na tabbatar wa al’ummar Jihar Katsina cewa NDLEA ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ci gaba da yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi da safararsu, tare da kira ga jama’a da su bayar da haɗin kai domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron al’umma a jihar.” Ya jaddada.
Kwamandan ya sanar da cewa hukumar ta NDLEA ta ɗaga matsayin jami’anta guda 61 a matakai daban-daban, ciki har da sauya wasu daga Non-Commissioned Officers zuwa Commissioned Officers, inda aka ɗaga jami’ai biyar daga matakin Anini ɗaya zuwa Anini biyu, tare da ɗaga wasu jami’ai 56 zuwa muƙamai daban-daban.
