Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Babban kotun jihar ƙarƙashin jagorancin Babban Jojin Jihar Katsina, mai Shari’a Musa Ɗanladi Abubakar, ta shirya taron horaswa da ƙara wayar da kai ga Alƙalai da lauyoyi kan ƙarfafa ilimin fasahar zamani (ICT), da fasahar wucin-gadi (Artificial Intelligence – AI) domin inganta aikin shari’a.
Taron ya mayar da hankali ne kan ƙarfafa ilimi a fannin fasahar zamani, tare da amfani da fasahar wucin-gadi (Artificial Intelligence – AI) da kuma sabbin kafafen sadarwa (New Media) wajen inganta gudanar da aikin shari’a.
Da yake gabatar da jawabin buɗe taron, babban jojin na Jihar Katsina, Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar, ya jaddada cewa sauyin zamani ya wajabta wa ɓangaren shari’a rungumar fasahar zamani domin sauƙaƙa aiki, hanzarta shari’u, tare da kare mutunci da martabar kotuna.
Ya kuma shawarci Alƙalan Majistare da su yi amfani da kafafen sadarwa cikin tsari tare da bin ƙa’idoji da dokokin aiki.
Farfesa Mainasara Yakubu Kurfi ya gabatar da takarda kan rawar da ɓangaren shari’a ke takawa a zamanin kafafen sada zumunta, inda ya bayyana hanyoyi da ƙa’idojin da suka dace da Alƙalai su bi wajen amfani da sabbin kafafen sadarwa, domin kare amincewar jama’a da martabar ɓangaren shari’a.
Haka zalika, Engr. Abbas ya yi bayani dalla-dalla kan ilimin fasahar eucin-gadi (Artificial Intelligence – AI).
Daga cikin waɗanda suka gabatar da jawabi yayin taron akwai shugaban matasa Media Links, Malam Ahmed Abdulkadir, , Dr. Basira Umar, da sauran masu ruwa da tsaki.
Taron wanda ya gudana a ɗakin taron Kotun, ya samu halartar manyan jami’an shari’a daga sassa daban-daban na Jihar Katsina.
