Neja: Al’umma sun shiga firgici bayan gano kan makami mai linzami na Amurka a wani ƙauye

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mazauna yankin Zugurma a Ƙaramar Hukumar Mashegu ta Jihar Neja sun shigar firgici a yau Litinin bayan gano wani abu mai kama da kan makami mai linzami a wani juji da ke kusa da su, lamarin da ya sa jami’an tsaro suka gaggauta kai ɗauki.

A cewar majiyoyi daga yankin, ‘yan ƙauyen ne suka ga baƙon abin a lokacin da suke gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Ganin haka ya sa suka hanzarta sanar da jami’an tsaro domin ɗaukar matakin gaggawa.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa manema labarai cewa ana zargin abin kan makami mai linzami ne da ake kyautata zaton yana daga cikin makaman da Amurka ta harbo a kwanakin baya. Saidai, ba a kai ga gano yanayi da kuma daga inda yake ba.

Da yake tabbatar al’amarin, Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya bayyana cewa an gano abin ne da misalin ƙarfe 2 na rana sakamakon kiran ujila daga yankin na Zugurma.

Akan haka ne Abiodun ya ce aka tura jami’an ‘yan sanda daga babban ofishin Ibbi zuwa wajen domin bada cikakken tsaro akan al’amarin.

A cewarsa, ‘yan sandan cikin ɗan ƙanƙanin lokaci suka zagaye yankin tare da tabbatar da ba al’ummar yankin tsaron da ya dace da kawar da dukkan abin da ka iya zama haɗari a gare su.

Kakakin ya ƙara da cewa, tuni jami’an kula da lamuran ababen fashewa suka kai abin ofishin hukumar domin gudanar da bincike a kai.

By Babaji