Da Ɗumi-Ɗumi: Chelsea ta naɗa sabon koci

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta naɗa Liam Rosenior a matsayin sabon mai horar da ‘yan wasanta, inda ta ba shi kwantiragin shekaru shida.

A sanarwar da ta fitar, Chelsea ta ce za ta cigaba da mayar da hankali akan inganta ‘yan wasa, yayin da take fatan cimma manyan burikanta.

A nasa ɓangaren, Rosenior ya bayyana alfaharinsa ga samun muƙamin wanda ya bayan a matsayin babban dama ga zangonsa na horarwa.

Ya ce, zai yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ƙungiyar ta cimma nasarori a yayin zamansa a muƙamin.

Tsohon ɗan wasan bayan ya ƙara da cewa, duk da cewa yana da alaƙa mai ƙarfi da tsohuwar ƙungiyarsa, damar horar da ‘yan wasan Chelsea ba abin ƙin amincewa ba ne.

By Babaji