Dakarun tsaro sun ceto tsohon soja daga hannun ‘yan bindiga a Filato

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jami’an Rundunar Sojoji ƙarƙashin sashen 3 da Operation Enduring Peace, sun yi nasarar ceto wani kanal mai ritaya mai suna Ajanaku daga komar ‘yan bindiga a Ƙaramar Hukumar Bassa da ke Jihar Filato.

A cewar masanin harkar tsaro, Zagazola Makama, an tsohon jami’in sojan ne a yankin Rafiki da ke ƙaramar hukumar, bayan bin diddigin ‘yan bindigar a Wildlife Park, wajen da suke bi su tsere.

Rundunar sojin ta tabbatar da cewa an samu nasarar ceton ne bayan haɗin-gwiwa da kuma gaggawar ɗaukar mataki daga jami’an tsaro, inda suka bi sawun masu aikata laifin tare da kara kaimi wajen bincike a yankunan da bayanan sirri suka bayyana.

Haka kuma, an ceto tsohon jami’in cikin aminci, inda aka kai shi cibiyar lafiya ta rundunar sojin domin duba lafiyarsa.

Jami’an tsaro sun bayyana cewa saurin ɗaukar mataki da tsare-tsaren sirri sun taimaka matuƙa wajen samun nasarar aikin.

Rundunar sojin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na sashen, Laftanal Kanal Aliyu Ɗanja, ta jaddada ƙudirinta na cigaba bada kariya ga rayuka da dukiyoyin al’umma tare da tabbatar da zaman lafiya a sassan ƙasar.

By Babaji