
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sanannen tauraron Soshiyal Mediya, Martins Vincent Otse da aka fi sani da VeryDarkMan ya janyo ce-ce-ku-ce bayan ya fito fili ya bayyana goyon bayansa ga tsohon gwamnan Jihar Kogi na tsayawa takarar sanatan Kogi ta Tsakiya a zaɓen 2027 da ke tafe.
A ranar 30 ga watan Disamba tsohon gwamnan ya bayyana muradinsa na tsayawa takarar kujerar sanata, a lokacin da ya ziyarci Fadar Ohinoyi na Masarautar Ebira.
A nan ne ya gabatar da jawabi ga sarakunan gargajiya, jagororin addini da sauran masu ruwa da tsaki na mazaɓar sanatan, inda ya ce ya karɓi ya fito takara.
Yahaya Bello, wanda a yanzu ake shari’ar zargin sa da hannu a badaƙalar kuɗaɗe, ya yi gwamna a Kogi daga shekarar 2016 zuwa 2024 kuma yana ɗaya daga cikin jiga-jigan Jam’iyyar APC a jihar..
A halin yanzu kujerar na hannun Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta Jam’iyyar PDP, wadda aka zaɓe ta a 2023, lamarin ta zama mace ta farko da ke wakiltar mazaɓar a Majalisar Dattawa.
A wani rubutu da ya wallafa a yau Talata, VeryDarkMan ya bayyana cewa duk da ƙalubalen siyasa da suka dabaibaye Yahaya Bello a baya musamman binciken da EFCC ta ƙaddamar akansa, hakan abu ne da ya taimaka masa wajen gyara kurakuransa da kuma ƙara samun ƙwarewa.
A cewarsa, tsohon gwamnan na buƙatar a ba shi wata dama a karo na biyu domin shimfiɗa ayyuka sama da waɗanda ya yi a baya a muƙamin da ya riƙe, yana mai cewa Natasha ba ta da ƙwarewa kamar sa.
