
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Aƙalla mutane 32 ne ‘yan bindiga suka yi awon-gaba da su ciki har da tsohuwa da ƙananan yara bayan sun halaka wasu guda biyu a Jihar Kaduna.
A cewar SaharaReporters, an sace tsohuwar ne ƙasa da kwana biyu da halaka babban ɗanta da wani a Ƙauyen Arak da ke Ƙaramar Hukumar Sanga.
Matar mai suna Misis Averik Arak, an sace ta ne tare da jikarta bayan halaka baban jikar mai suna Habila Averik a ranar Lahadi.
An ruwaito cewa, dattijuwar ta shiga halin rashin lafiya sakamakon kashe ɗanta a kan idonta tare da mata da ‘yarsa, inda a yammacin Litinin ne ‘yan bindigar suka sake komawa ƙauyen.
Haka ma a wani hari makamancin wannan a ƙananan hukumomin Kauru da Kajuru, inda aka yi garkuwa da mutane 15 waɗanda galibinsu ƙananan yara ne daga Unguwar Sarkin Maro. A ƙauyen Kadage na Kauru, an sace mutane 16 da halaka ɗaya.
Wata majiya daga Kadage ta ce sama da ‘yan uwansu guda 100 ke hannun ‘yan bindiga tun daga ranar 1 ga watan Disambar 2025 zuwa 4 ga watan Junairu.
Ta kuma koka ga yadda gidajen jaridu suka ɗauke ƙafa ga bayyana ayyukan sace-sacen ɗan-adam da ya dawo wa yankin nasu.
Da fari SaharaReporters ta ruwaito cewa ‘yan ta’adda sun kashe ‘yan gida ɗaya a garin Kachia da ke Kudancin Kadunaa a ranar Juma’a yayin wani hari da suka kai cikin dare.
