Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Wannan wasiƙa an rubuta ta ne domin mu tsaya mu yi nazari mai zurfi a kan inda muka fito, inda muke, da kuma inda muke son zuwa. Shekara ta 2025 ta ƙare, kuma 2026 na tafe da sabuwar dama, sabuwar jarrabawa, da sabbin alhakin da za su rataya a wuyan kowannenmu. Tambayar da ta dace mu yi wa kanmu ita ce: me mu ke yi a 2025 da zai zama ginshiƙin alkhairi a 2026?
Rayuwa tana gudu ba tare da jiran kowa ba. Ranaku suna shuɗewa kamar iska, watanni suna biye wa juna, shekaru kuma suna zamewa ba tare da mun ankara ba. Abin tausayi shi ne, da yawa daga cikinmu muna cika kwanaki ne ba tare da mun cika rayuwa da ma’ana ba. Muna tashi muna kwana, muna cin abinci muna sha, amma ba lallai ne muna rayuwa yadda ya dace ba. Wannan wasiƙa kira ce gare mu baki ɗaya da mu farka daga barcin sakaci.
Shekara ta 2025 ta nuna mana abubuwa da dama. Ta nuna mana cewa duniya ba ta da tabbas. Ta nuna mana cewa arziki na iya canjawa a ƙiftawar ido, lafiya na iya juya zuwa rashin lafiya, farin ciki na iya koma baƙin ciki. Ta kuma nuna mana cewa mutuwa ba ta da lokacin da ta ke jira. Ba tsoho kawai ke mutuwa ba. Matasa suna mutuwa. Yara suna mutuwa. Masu ƙarfi da masu rauni duk suna barin duniya. Wannan gaskiya ce mai zafi, amma wajibi ne mu rungume ta domin ta gyara mana tunani.
Idan muka fahimci cewa mutuwa kusa take, to halayyenmu za su canja. Zancenmu zai gyaru. Mu’amalarmu da mutane za ta inganta. Zuciyarmu za ta yi laushi. Za mu daina cutarwa da zalunci. Za mu rage hassada da ƙiyayya. Za mu fara tambayar kanmu: idan na mutu yau, me zan tarar gobe?
Al’umma ba ta gyaruwa sai idan ɗaiɗaikun mutane sun gyaru. Ba za mu iya jiran gwamnati ko shugabanni kawai su gyara mana komai ba. Kowa na da rawar da zai taka. A 2026, mu fara da kanmu. Mu gyara zuciyarmu kafin mu gyara harshenmu. Mu gyara niyyarmu kafin mu gyara ayyukanmu. Ayyukan alkhari ba lallai sai manya ba. ƙaramin alkhari ma yana da girma a wajen Allah da kuma a idon al’umma.
A 2026, mu riƙa tausaya wa juna. Mu daina jin daɗin ganin wani ya faɗi ko ya shiga matsala. Mu riƙa taimako gwargwadon iko, ko da kalma ce mai daɗi, ko sanya wani murmushi, ko addu’a ce daga zuciya. Wasu mutane ba kuɗi suke nema ba, kulawa suke nema. Wasu ba abinci suke nema ba, girmamawa suke nema. Idan muka koya wa kanmu waɗannan ɗabi’u, al’umma za ta sauya.
Halayyen na kwarai su ne tubalin kowace al’umma mai ƙwari. Gaskiya, amana, haƙuri, tawali’u, da adalci su ne ginshiƙar zaman lafiya. Ba za mu iya gina makoma mai kyau ba idan mun cika da ƙarya, cin amana, girman kai da zalunci. 2026 ta zama shekarar da za mu yi alƙawari da kanmu cewa za mu tsaya a kan gaskiya, ko da ta yi mana zafi.
Mu kuma tuna da alhakin da ke kanmu a matsayin iyaye, ’ya’ya, ‘yan uwa da ‘yan ƙasa. Yaranmu suna koyo ne daga abin da suke gani, ba daga abin da muke faɗa kawai ba. Idan muna son su zama nagari, dole mu zama abin koyi. Idan muna son su ji tsoron Allah, dole mu nuna musu a aikace. Idan muna son su zama masu mutunci, dole mu girmama mutane a gaban su.
Wasiƙar nan ba wai tsoratarwa ce kawai ba. Kira ce ta bege. Duk da yawan matsaloli, har yanzu muna da damar gyaruwa. Duk wanda ke da numfashi, yana da dama. Allah Mai rahama ne, yana karɓar tuba, yana son alkhairi ga bayinsa. Amma ba za mu yi wasa da lokaci ba. Abin da za mu yi yau ya fi sauƙi fiye da abin da za mu yi gobe.
A 2026, mu rage husuma. Mu nemi gafara daga wanda muka cuta. Mu yafe wa wanda ya cuce mu. Ba rauni ba ne yafe wa mutane, ƙarfi ne. Zuciya mai nauyin ƙiyayya ba ta iya tafiya nesa. Idan muna son samun natsuwa da salama, dole mu koyi sakin nauyin da ke zuciyarmu.
Mu kuma tuna cewa duniya hanya ce, ba gida ba. Duk abin da muke tarawa za mu bari. Duk muƙami da suna za su tsaya a nan. Abin da kawai zai bi mu shi ne ayyukanmu. Wannan ya sa ya dace mu tambayi kanmu tun a 2025: wane irin kaya nake tanadawa domin tafiyar da ba ta da dawowa?
Ina kira ga malamai, ‘yan kasuwa, ɗalibai, ma’aikata, shugabanni da talakawa: mu yi anfani da 2026 wajen gina kanmu da al’ummarmu. Mu riƙa koyar da alkhari, mu riƙa faɗin gaskiya, mu riƙa tsayawa kan adalci. Ko da ba kowa zai yarda da mu ba, Allah zai yarda.
A ƙarshen wannan wasiƙa, ina roƙon kowa da kowa ya yi tunani mai zurfi a zuciyarsa. Kada mu bari 2026 ta zo ta wuce kamar sauran shekarun da suka gabata ba tare da wani canji na zahiri ba. Mu sanya wa kanmu alƙibla. Mu sanya wa kanmu manufa. Mu yi rayuwa da niyya, ba da sakaci ba.
Allah Ya sa mu dace, Ya gyara zukatanmu, Ya sa mu kasance masu anfanar kanmu da al’ummarmu. Ya sa mu riƙa tunawa da mutuwa a kowane lokaci domin ta zama haske ba duhu ba. Idan muka yi hakan, to lallai 2026 za ta zama shekarar alkhari, gyara da fata mai kyau.
Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD, ƙaramin Edita, Blueprint Manhaja. 07066778190.
