
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Al’amuran siyasa a Jihar Ribas da ke kudancin ƙasar nan na shirin ɗaukar wani salo, yayin da Majalisar Dokokin jihar ta fara shirye-shiryen tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Oduh.
A yayin zaman na yau Alhamis ƙarƙashin jagorancin Kakakinta, Martins Amaewhule, majalisar ta bakin jagoran mafiya rinjaye, Major Jack, ta karanta wani saƙon gargaɗi da ke zargin gwamnan da saɓa wa ƙa’idojin aiki.
Tuni ‘yan majalisar guda 26 suka goyi bayan saƙon, inda suka yi ikirarin gwamnan ya aikata wasu laifuka da suka saɓa wa dokokin Nijeriya.
Hon. Amaewhule ya bayyana cewa za a miƙa wa Fubara takardar acikin kwanaki bakwai.
Haka ma mataimakiyar jagoran mafiya rinjaye, wato Linda Stewart, wadda ita ta karanta saƙon zarge-zargen saɓa wa sharuɗɗan aiki akan mataimakiyar gwamnan, Ngozi Oduh.

