
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja ta umarci a karɓe kadarori guda 57 da aka yi zargin suna da alaƙa da tsohon Antoni-Janar kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami da ‘ya’yansa biyu, wato Abdulaziz da Abiru-Rahman tare da damƙa wa Gwamnatin Tarayya.
Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Laraba, inda ta ce tana kuma zargin an mallake su ne waɗanda suka haɗa da gidaje da filaye ta haramtattun hanyoyi.
Mai shari’a Emeka Nwite ne ya yanke hukuncin bayan lauyan hukumar EFCC, Ekele Iheanacho ya buƙaci hakan.
A wata sanarwa da EFCC ta fitar, ta ce an ƙiyasta darajar kadarorin za ta kai N213,234,120,000 da ya mallaka a jihohin Kebbi, Kano, Kaduna da kuma Abuja.
Ta kuma umarci da a wallafa hukuncin ƙwace su na wucin-gadi, tana mai kira ga “duk wanda da ke da alaƙa da kadarorin kuma yake ganin bai kamata a ƙwace na dindindin a miƙa wa gwamnatin tarayya ba da ya fito ya yi bayani a cikin kwana 14.”
Baya ga haka ne alƙalin ya ɗage shari’ar zuwa ranar 27 ga watan Janairu domin cigaba da zama a kai.
