2027: Ministan Labarai ya dakatar da mai taimaka masa bayan musanta fitowa takarar gwamna

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, ya dakatar da ɗaya daga cikin mataimakansa mai suna Sa’idu Enagi bisa tsokacinsa na cewa akwai yiwuwar ministan ya tsaya takarar gwamna a Jihar Neja yayin zaɓen 2027.

Mai taimaka wa ministan akan harkokin yaɗa labarai Rabi’u Ibrahim ne ya bayyana haka a wata takarda, inda ya kuma yi kira ga al’umma da su yi watsi batun, wanda a cewarsa, ba daga ministan ba ne.

Mohammed Idris ya ce, a yanzu ya mayar da hankalinsa ne wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa na sanar da ‘yan Nijeriya batutuwan da suka shafi tsare-tsare da shirye-shiryen gwamnati, don haka ba shi da lokacin siyasa.

Ya ƙara da cewa, yana jin daɗin kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninsa da Gwamna Mohammed Umaru Bago na Neja domin amfanin jihar, inda yake ganin batu irin haka ka iya kawo cikas ga ci-gaban jihar.

Saboda haka ne ya kirayi al’umma da su ƙaurace wa zancen, wanda ba da yawunsa aka yaɗa ba.

Kazalika, ya umarci da a gaggauta gudanar da binciken akan dakataccen jami’in akan al’amarin.

By Babaji