
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnan Tarayya ta ƙaryata rahotannin da ke yawo a wasu kafafen labarai game da ɗaliban da suka samu damar karatu kyauta a ƙasar Moroko, tana mai bayyana ikirarin a matsayin ƙarya mara tushe da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da jama’a.
A wata sanarwa ta ranar Laraba daga Daraktar hulɗa da jama’ar Ma’aikatar Ilimi, Boriowo Folasade, Minista Dakta Tunji Alausa ya bayyana cewa, babu wani ɗalibin Nijeriya da ke ƙarƙashin halastaccen shirin karatu kyauta da aka yi watsi da shi.
Ya ce, dukkan ɗaliban da ke cikin tsarin karatun da aka tantance su a shirin ‘Bilateral Education Scholarship’ (BES) tun gabanin 2024, an biya su kuɗaɗen da aka yi musu alƙawari, wanda yana daga cikin kasafin 2024 kamar yadda gwamnatin ta tanada.
Dakta Alausa ya kuma ce dukkan wani abu da zai haifar da tsaiko wajen biya musamman na abin da ya shafi jinkiri, an warware shi ta hanyar aiki tsakanin Ma’aikatar Ilimi da ta Kuɗi.
Ministan ya ƙara da cewa, daga watan Oktoban 2025 zuwa yanzu babu wani sabon ɗauka da aka yi na karatun ɗalibai kyauta.
Kazalika, ya bayyana cewa matakin gwamnati na rashin cigaba da ɗaukar nauyin karatu kyauta ga wasu tsare-tsare ya samu ne sakamakon nazari akan tsarin, wanda ya gano cewa manyan makarantun Nijeriya sun wadaci dukkan ‘yan Nijeriya a yanzu duba da bunƙasarsu a ‘yan shekarun baya-bayan nan.
Don haka tsarin ɗaukar nauyin karatu da ke ƙarƙashin gwamnatocin waje ne kaɗai ake tallafa wa da dukkan abin da ya dace daga gare su, kamar yadda ya shaida.
A ƙarshe, Ministan ya ce gwamnati tana aiki tuƙuru wajen ganin ta kawara da dukkan rashin tsari da ababen da ke haddasa tsaiko a harkar karatu kyauta na gwamnatin ƙasar.
