Yadda aka gudanar da taron ranar marubuta Hausa ta duniya a Jigawa

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Jigawa

Haɗakar ƙungiyar ƙungiyoyin marubuta ta Nijeriya ta gudanar da taron ranar marubutan Hausa ta duniya, da ya gudana a Jihar Jigawa, ranar Laraba 31 ga Disambar 2025.

Taron wanda aka assasa shi domin al’amura da harkokin marubuta, da kuma bajekolin fasahohin marubuta da littattafai.

Kabir Yusuf Anka shi ne mai magana da yawun babban kwamitin shirya taron, ya bayyana cewa manufar shirya taron shi ne sada zumunci da haɗuwa da juna da buɗe ido.

Ya ce taron ya kasance ana tattaunawa rubuce-rubucen ƙagaggun labarai na Hausa da al’adu da harshe da tarihi duka na Hausawa.

Sannan ya ce “Ana yin karance-karancen ƙagaggun labarai da gabatar da takardu da muƙalu da suka shafi fasahohin marubuta da rubutu da cigaban zamani, musamman AI.

“Sannan an bayar da kyaututtukan gasannin ƙagaggun labarai da aka yi na shekara 2025”. In ji Kabiru Fagge

Taken taron na bana dai shi ne: Marubuta a Ƙarni Na 21: Ƙalubalen tsaro da Tattalin arziki

Farfesa Mu’azu Muhammad Kudan malami ne a jami’ar Sule Lamido da ke Kafin Hausa ya bayyana cewa da alƙalamin marubuci ana iya sarrafa duniya da daƙile matsaloli ta hanyar fito da daga ina aka saki layi aka shiga daji, ya ƙara da cewa.

“Idan har marubuci zai yi amfani da idon zuciya da zaren tunani ya ƙulla hanyoyin da ake samu a fahimci baƙo da halin bako sannan kuma da muhallin da ya zo mai ya kawo shi kuma yaushe zai bar gurin wannan zai sa su mazauna gurin su kyautata zamantakewa kuma su sa ido akansa”.

“Amma zaman kara zube ba ruwan wani da wani shi yake ƙara kawo rikici a tsakaninmu, sannan sai mun rage son abin duniya shi kansa yana ƙara kawo mana son abin duniya” a cewar Farfesa Kudan.

Shi ma a nasa jawabin, tsohon shugaban ƙungiyar marubuta ta ANA reshen Jihar Kano, kuma Sarkin Mawallafa na Arewa Mal. Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya bayyana cewa duk da ƙalubalen da ake fuskanta na rashin tsaro, to akwai kuma dabi’ar nan ta rashin yin karatu musamman a tsakanin matasa, inda ya ce abu ne da yake buƙatar miƙewa tsaye wajen magance matsalar, ta hanyar canza tunanin al’umma tun daga makarantu.

“Malaman makarantu su dinga kafa masu kulob-kulob na karatu da al’adu sannan su dinga kiran marubuta suna yi wa ɗaliban bita kan muhimmancin yin rubutu da muhimmancin karanta littafai hakan zai sa a cigaba da haɓaka harshe” inji Ado Gidan Dabino

Taron wanda ake gudanar da shi duk shekara biyar zuwa sama, ya samu halarta marubuta sama da 300 a faɗin Nijeriya kuma samu wakilci gwamnatocin Arewa da dama musamman ma Kano, Katsina da Jigawa. Sannan an samu halartar manyan baƙi daga ƙasashen Togo da Kamaru da kuma Nijar da sauransu.

By ukarofi