Waƙa: Ina muka dosa?

Spread the love

Daga BALA MUHAMMED GARBA

1.Rabbana yankin Arewa,

   Kullu-yaumin ai kashewa,

 Ba mu san usulin hakan ba.

2.  

  Rabbi an kashe Tajiranmu,

Kuma an kashe Malamanmu,      

         Har Sarakai ba a bari ba.

3.

  Makarantu an rufe su,

 Kasuwanni an kashe su,

 Me ya sa ba zan koka ba?

4.

Ga shi an rusa tarbiyyarmu,

   Kana an raba al’ummarmu,

Ba mu san manufar hakan ba.

5.

Yau da namu ake kashe mu,

          Su ake sa sui satar mu,

        Har kuɗin fansa su karɓa.

6.  

     Da a ce ba a kashe mu,

 Babu wanda yake taɓa mu,

     Da ba za nayi baitukan ba.

7.  

       Da a ce ba a sace mu,

    Duk ana noma yankinmu,

      Da ba za nayi magana ba.

8.

  Da Manoma da Makiyayya,

   Zaune lau suke babu kayya,

      Da ba za fa kusan da ni ba.

9.  

Da ‘ya’yanmu su na karatu,

 Ba su maye duk an wadatu,

     Da ba za ku ji nai waƙa ba.

10.

    Da Arewa kalau take yau,

Duka zaune marau muke mau,

        To ba za ku ji mai na ce ba.

11.

Yanzu dubi kamar Fulani,

Sai su sace mutum a birni,

   Har kuɗin fansa su karɓa.

12.

  Da muna da tsaro Arewa,

   Ga ruwan sha bai ƙafewa,

   Da ba zan magana a kai ba.

13.

Tun da an taɓa yakunanmu,

Kana an kashe ‘yan uwanmu,

     Ai ba zan yi shuru a kai ba.

14.

    Tun da ni waƙa nake yi,

Kuma ba ni da yadda zan yi,

        Ai ba za na ƙi baituka ba.

15.

Duka an rufe bakunanmu,

Kuma ga shi ana kashe mu,

Kai! Ba zan fa shuru a kai ba. 

16.

   Da da masu faɗa Arewa,

      Da da ‘yan kishin Arewa,

          Da hawaye bai zube ba.

17.

 Da da babba cikin Arewa,

    Mai faɗa a ji ba musawa,

    Da ba za ya ƙi magana ba.

18.

Da su Ahmadu Bello na nan,

  Ko Taɓawa yana ƙasar nan,

           Da Arewa ba ta ƙafe ba.

19.

Da su Murtala na a raye!

 Ko Abacha yana a ƙauye!

 Da ba a kashe al’umma ba.

20.

Da Hassan Katsina yana nan,

       Maimalari yana ƙasar nan,

     Da ba za mu zamo hakan ba.

21.

Da su Elkanemi su na nan,

   Ko Aminu Kano yana nan,

  Da ba zai yi shuru kawai ba.

22.

     Da su Shehu na a raye,

Malamai na Madabo tsaye,

      Da ba a raba al’umma ba.

23.

 Tun da mun yi rashin iyaye,

Kuma ga mu dukanmu maye,         

      Ai ba za mu ƙi tamɓara ba.

24.

Tun da yau ba wani babba,

  Wanda zai yi hani da gaba,

        To ta ya za mu ci gabba?

25.

  Da da babba cikin Sarakai,

Wanda zai yi kiran haɗin kai,

     Da ba za mu ƙi bin kiran ba.

26.

Jallah ceci dukan Arewa,

Rabbi ba mu da mai iyawa,

  Don Rasulu riƙon Suwaiba.

27.

Rabbana don mai kiyama,

 Sa mu zaunu cikin salama,

    Jallah ba don ni ba Rabba.

28.

  Rabbana ka daɗo salatai,

Har ya zarce yawan halittai,

   Ahlul Baiti ka sa su Rabba.

29.

ɗanbala daga Borno ne ni,

             Ɗalibi kar ku kira ni,

     Malami ban kai hakan ba.

30.

Litinin ga watan Disambar,

 Ran ɗaya ga wata na bayar,

   Twenty twenty-fiɓe ku duba.

By ukarofi