Shekarun baya-bayan nan sun kasance masu cike da jarrabawa ga ’yan Nijeriya. Bayan zazzafar siyasar zaɓen 2023 da kuma ƙalubalen tsaro da tattalin arziki da suka biyo baya, shekarar 2025 ma ta zo da nata nauyin – daga hauhawar farashi, tsadar rayuwa, zuwa matsalolin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar nan. Yanzu da aka shiga shekarar 2026, al’umma na sa ran ganin sauyi na gaskiya, wanda zai tabbatar musu cewa dimokuraɗiyya da shugabanci na iya kawo sauƙi a rayuwarsu.
Abu na farko da ke gabansu shi ne gyaran tsarin zaɓe. Duk da kiraye-kirayen da aka yi bayan babban zaɓen 2023, har yanzu akwai giɓi a amincin jama’a ga yadda ake gudanar da zaɓuka. Amfani da na’urorin tantance masu kaɗa ƙuri’a da watsa sakamako ta hanyar lantarki ya nuna haske, amma matsalolin sadarwa da rashin cikakken bin doka sun raunana tasirinsa. A shekarar 2026, ’yan Nijeriya na son a gyara dokar zaɓe ta yadda za ta wajabta amfani da fasahar zamani daga rumfunan zaɓe har zuwa tattara sakamako ba tare da katsalandan ba.
Har ila yau, jama’a na kira da a sake duba sharuɗɗan cin nasara a zaɓuka. Zaɓen shugaban ƙasa da gwamnonin da ke gudana da ƙuri’u marasa rinjaye na barin mutane da tambayoyi kan sahihancin wakilci. ’Yan Nijeriya na son a samar da tsarin zagaye na biyu idan babu wanda ya samu aƙalla kashi 50 cikin 100 na ƙuri’u, domin tabbatar da cewa shugabanni sun samu cikakken goyon bayan jama’a.
Batun shari’a ma ya zama ginshiƙi a wannan fata. Jama’a na son a rika kammala dukkan ƙararrakin zaɓe kafin rantsar da waɗanda aka ayyana a matsayin masu nasara. Haka kuma ana kira da a bai wa INEC cikakken ‘yancin kai wajen naɗa jami’anta, domin kawar da zargin ɓangaranci da katsalandan na siyasa.
A ɓangaren tsaro, wannan na daga cikin manyan damuwar ’yan Nijeriya a 2026. Hare-haren ’yan bindiga, sace-sace, fashi da makami da garkuwa da mutane sun ci gaba da addabar al’umma. Jama’a na buƙatar hukumomin tsaro masu ƙwarewa, tare da amfani da bayanan sirri da fasahar zamani wajen hana aikata laifi, ba wai jira sai an kai hari ba. Idan ba a yi garambawul ba, tsoron fita gonaki, tafiya kan manyan hanyoyi da zama lafiya a gidaje zai ci gaba da kasancewa barazana.
Tattalin arziki kuma ya tsaya a zuciyar wannan fata. Duk da wasu gyare-gyare da gwamnati ke iƙirarin yi, hauhawar farashin kaya da tsadar rayuwa sun sanya rayuwa ta yi wa talakawa tsauri. Miliyoyin ’yan Nijeriya na fama da talauci, suna ƙasa biyan buƙatun yau da kullum. A 2026, jama’a na son gwamnati ta samar da manufofi masu rage tsadar abinci, inganta wutar lantarki, tallafa wa manoma da ƙananan ’yan kasuwa, domin farfaɗo da tattalin arziki daga tushe.
Baya ga haka, ’yan Nijeriya na kira da shugabanni su nuna gaskiya da riƙon amana. Ba za a ce talakawa su yi haƙuri da tsadar rayuwa ba, alhali shugabanni na rayuwa cikin almubazzaranci. Jama’a na buƙatar shugabanci mai tausayi, wanda ke fahimtar halin da mutane ke ciki.
Majalisar Dokoki ma ana son ta dawo kan turbar aikinta ta gaskiya – ta sa ido kan ɓangaren zartarwa da na shari’a ba tare da nuna son kai ba. Haka kuma, ana buƙatar rage dogaro da bashin ƙasashen waje, domin kusan dukkan kuɗin shigar ƙasa na tafiya wajen biyan basussuka. Maimakon haka, ya kamata gwamnati ta samar da hanyoyin samun kuɗaɗen shiga na cikin gida, ta hanyar haɓaka masana’antu, noma da harkokin kasuwanci.
A ƙarshe, ’yan Nijeriya na son a bai wa ƙananan hukumomi cikakken iko da kuɗaɗen da suka dace, domin su iya kawo cigaba kai tsaye ga jama’a a matakin ƙasa. Rarraba iko yadda ya kamata shi ne ginshiƙin dimukuraɗiyya ta gaskiya.
A matsayinmu na jarida, muna yi wa ’yan Nijeriya fatan samun sauyi na ainihi a shekarar 2026 – sauyin da zai tabbatar da cewa wahalhalun da suka sha a baya ba su tafi a banza ba. Nijeriya na da albarka da dama, abin da ake buƙata kawai shi ne shugabanci na gari, gaskiya da kishin ƙasa.
