Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wasu ɗaliban Nijeriya da ke karatu a Moroko a ƙarƙashin shirin tallafin karatu na Gwamnatin Tarayya sun bayyana halin da suke ciki, inda suka ce tsawon watanni, kusan ma da shekaru ana watsi da su ba tare da kulawa ba, lamarin da ya jefa da dama cikin yunwa, rashin matsuguni da kuma tangarɗar samun kulawar lafiya.
A wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta ranar Talata, an ga mai sukar al’amuran gwamnati a kafafen sada zumunta, ɓincent Martins Otse, wanda aka fi sani da ɓDM, yana tattaunawa da wasu daga cikin ɗaliban Nijeriya da suka maƙale a Moroko.
ɗaliban sun bayyana cewa duk da kasancewarsu masu cin gajiyar tallafin karatu na gwamnatin Nijeriya, an barsu ba tare da tallafin kuɗi ba tsawon lokaci.
Yayin da yake magana a bidiyon, ɓDM ya zargi gwamnatin Tarayya da gazawa, yana mai cewa zaliban da aka tura Moroko domin karatu sun zama marasa aikin yi kuma sun rasa mafita saboda watsi da aka yi da su. Ya ce al’amarin ya nuna yadda aka gaza cika alƙawuran da aka ɗauka a kansu.
Wasu daga cikin ɗaliban da suka yi magana sun bayyana cewa an hana su yin aiki domin neman abin dogaro, bisa yarjejeniyar da ke tsakanin gwamnatocin ƙasashen biyu. Sun ce hakan ya ƙara tsananta musu rayuwa, ganin cewa babu tallafin da ake biyan su.
Wani ɗalibi da ya ce yana shekararsa ta ƙarshe a fannin likitanci ya bayyana cewa sun shafe shekaru suna karatu da burin komawa Nijeriya domin taimaka wa ɓangaren lafiya, amma aka barsu cikin hali na ƙunci. Ya ce an yi musu alƙawarin tallafi amma bai taɓa zuwa ba.
Wani ɗalibi da aka gani yana tafiya da sanduna ya ba da labarin yadda tsananin buƙata ya tilasta masa yin aiki a ɓoye, duk da haramcin yarjejeniyar. Ya ce a kan hanyarsa ta dawowa daga aikin ne ya yi hatsari ya karya cinyarsa, kuma tun daga lokacin bai iya biyan kuɗin asibiti ba saboda rashin kuɗi.
ɗaliban sun kuma yi bayani kan rasuwar wani abokinsu, Bashir Malami, wanda yake ɗalibi a ƙarƙashin shirin BEA na shekarar karatu ta 2019/2020, a fannin injiniyancin lantarki a Ecole Superieure de Technologie de Sale. A cewarsu, Malami ya kamu da tarin fuka, amma ya ɓoye rashin lafiyarsa saboda tsoron kuɗin asibiti, lamarin da ya kai ga rasuwarsa.
Sun ce duk da cewa ana cewa magani kyauta ne a Moroko, rashin kuɗi da tallafi ya hana shi samun taimako cikin lokaci. ɗaliban sun ƙara da cewa an yi musu alƙawarin alawus na dala 500 a kowane wata, tare da biyan kuɗin jirginsu na farko zuwa Moroko, kuma sun yi iƙirarin cewa takardun tallafin sun fito ne daga ma’aikatar ilimi ta Tarayya.
A cewarsu, duk lokacin da suka yi barazanar kai ƙorafi ga manema labarai, ana zarginsu da ƙoƙarin kunyata gwamnati. ɗaya daga cikinsu ya ce abin da ya fi kunyatawa shi ne korar ɗalibai daga gidajen haya saboda rashin biyan kuɗi.
ɗaliban sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta ɗaukar mataki, suna gargaɗin cewa idan halin ya ci gaba, rayuka da makomar karatun ɗalibai da dama na cikin haɗari. Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, gwamnatin Nijeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan koken ɗaliban ba.
