Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kamus na Oxford (Oxford English Dictionary – OED) ya sabunta kundinsa inda ya saka wasu kalmomin asalin Nijeriya, ciki har da “abeg”, “moi moi”, “amala”, “nyash” da “mammy market”, a matsayin wata shaida ta ƙaruwar tasirin harshe da al’adar Nijeriya a duniya.
Rahoton da News Point Nigeria ta wallafa ya nuna cewa sabuntawar watan Disambar 2025 ta ƙara fiye da kalmomi da jimloli 500, tare da sabunta bayanan sama da kalmomi 1,000 da suka riga suna cikin ƙamus ɗin.
Editocin OED sun ce wannan sabuntawa na nuna yadda Ingilishi daga sassa daban-daban na duniya, ciki har da Afirka ta Yamma, ke ƙara samun karɓuwa a faɗin duniya.
Daga cikin sabbin kalmomin da aka ƙara akwai “abeg”, wanda kamus ɗin ya bayyana a matsayin kalmar da ake amfani da ita wajen nuna ban-haƙuri ko damuwa. Haka kuma “biko”, wadda asali kalma ce ta harshen Igbo, an bayyana ta a matsayin kalmar neman alfarma ko roƙo cikin ladabi, wato “don Allah”.
=Ƙamus ɗin ya kuma saka “nyash”, wadda aka fassara da ƙashin baya na mutum, musamman mata, yayin da “Ghana Must Go” ke nuni da shahararrun jakunkunan roba masu launin cakuɗa, da aka fi amfani da su wajen ɗaukar kaya a Afirka ta Yamma. Kalmar ta samo asali ne tun daga shekarar 1983 lokacin da Nijeriya ta kori ‘yan Ghana marasa takardun zama.
A ɓangaren abinci kuma, OED ya saka “amala”, wadda ake yi daga garin doya ko rogo, tare da “moi moi”, abincin wake da aka niƙa, aka haɗa da albasa da barkono, wanda ya shahara musamman a yankin Yarbawa.
Baya ga kalmomin Nijeriya, sabuntawar ta kuma haɗa da kalmomin yanar gizo kamar “DM”, “brainfart” da “chug”, tare da kalmar “Afrobeats” da aka bayyana a matsayin salon waƙar zamani da ke ɗauke da sassan waƙoƙin Afirka ta Yamma, jazz, soul da funk.
Editocin OED sun bayyana cewa sun kuma duba tarihin kalmomi kamar “troll”, “coffee” da “snooker”, a wani yunkuri na ƙara fahimtar yadda harshe ke sauyawa da kuma karɓuwa a sassa daban-daban na duniya.
A watan Janairun 2025, kamus ɗin ya riga ya saka kalmomi fiye da 20 daga Nijeriya, ciki har da “japa”, “agbero”, “eba”, “419” da “abi”, abin da ke nuna yadda Ingilishi na Nijeriya, Pidgin da harshen tituna ke ƙara tasiri a duniya.
Masana harshe na ganin wannan ci gaba a matsayin wata babbar nasara ga Nijeriya, domin yana tabbatar da yadda al’ada, harshe da rayuwar yau da kullum ke zama wani ɓangare na tsarin duniya.
