CIA da KGB sun ɗauki nauyin ƙungiyoyin ƙwadago don raunana Nijeriya – Obasanjo

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa a wani lokaci a tarihin Nijeriya, ƙungiyoyin ƙwadago sun faɗa cikin tasirin siyasar Yaƙin Cacar Baki, inda wasu ɓangarori ke samun ɗaukar nauyi daga Hukumar Leƙen Asiri ta Amurka (CIA) yayin da wasu kuma ke karɓar tallafi daga KGB ta tsohuwar Tarayyar Soɓiet.

Obasanjo ya bayyana haka ne a Abuja yayin bikin cika shekaru 85 da haihuwa da kuma aaddamar da littafin tsohon shugaban NLC, Hassan Sunmonu.

Taron ya samu halartar manyan jagororin ƙwadago, tsofaffin shugabanni da kuma ‘yan siyasa daga sassa daban-daban na ƙasar.

Tsohon shugaban ƙasar ya ce, wannan lamari ya zama babbar barazana ga ’yancin kai da tsaron Nijeriya, wanda hakan ya sa gwamnatinsa ta soja a wancan lokaci ta ɗauki matakan gyara tsarin ƙungiyoyin ƙwadago domin kawar da tasirin ƙasashen waje.

A cewarsa, “Gaskiya ne, wani ɓangare na ƙwadago KGB ke ɗaukar nauyinsa, wani kuma CIA. Sai na ce dole Nijeriya ta samu ƙungiyar ƙwadago da ‘yan Nijeriya ke shirya ta, suke jagoranta kuma suke ɗaukar nauyinta.”

Obasanjo ya bayyana cewa ya naɗa Mai shari’a Adebiyi domin jagorantar kwamitin da zai sake fasalin dokokin kwadago, duk da adawar da wasu shugabannin ƙwadago suka nuna a lokacin, ciki har da Hassan Sunmonu.

Ya ce bayan kammala aikin gyara dokokin da kafa NLC, gwamnati ta nesanta kanta daga tsoma baki a zaɓen shugabannin ƙungiyar.

“Ba tare da sa hannun gwamnati ba, su da kansu suka zaɓi shugabansu, kuma Hassan ya zama shugaban farko. Wannan ya sa na ji daɗin yadda aka gudanar,” inji Obasanjo.

Tsohon shugaban ƙasar ya kuma bayyana cewa ya shawarci Sunmonu da ya riƙa sukar gwamnati a fili idan ya ga dama, domin ya tabbatar wa ma’aikata cewa ƙungiyar na da ’yanci.

Ya ƙara da cewa, tsarin cire kuɗin rajista kai tsaye daga albashin ma’aikata (check-off system) ya taimaka wajen tabbatar da samun kuɗaɗen shiga na cikin gida, tare da katse dogaro da tallafin ƙasashen waje.

A taron, tsohon shugaban NLC kuma Sanata, Adams Oshiomhole, ya sha alwashin ci gaba da kasancewa tare da ƙungiyar ƙwadago har ƙarshe, yana mai kira ga ƙungiyoyi da su riƙa tsayawa tsayin daka wajen kare muradun ma’aikata.

Shugaban NLC na yanzu, Joe Ajaero, ya yi amfani da damar wajen sukar sabbin dokokin haraji na gwamnati, yana mai cewa suna cutar da ma’aikata da talakawa. Ya kuma zargi gwamnati da ware ƙungiyoyin ƙwadago daga tattaunawa kan sauye-sauyen haraji, lamarin da ya ce na iya haifar da rashin amincewa da tsaro a ƙasa.

Lauyan kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana, SAN, ya buƙaci shugabannin ƙwadago na yanzu da su yi koyi da irin nagartar shugabancin Sunmonu, yana mai tuna cewa sama da kashi 60 cikin 100 na ’yan Nijeriya na fama da talauci mai tsanani.

By ukarofi