
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wata Babbar Kotu a Jihar Jigawa, ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani mai suna Abubakar Muhd da aka fi sani da Akuya, bayan samun sa da laifin lalata da wani ɗan shekara 15.
Haka kuma ta umarce shi da ya biya diyyar Naira miliyan 5 ga yaron da ya yi wa abin da ta kira da ‘fyaɗe’.
Rahotanni sun bayyana cewa a watan Maris ɗin 2022 ne aka shigar da ƙarar, amma sai yanzu aka gurfanar da shi gaban kotu saboda wasu dalilai ciki har da bukatar ƙarin shaidu akan al’amarin.
Da yake gabatar da hukuncin a ranar Alhamis, Alƙalin kotun, Mai shari’a Ado Yusif Birnin Kudu, ya samu Muhd da laifin yi wa wani yaro daga Ƙauyen Nomi a Ƙaramar Hukumar Taura da ke jihar fyaɗe.
Da fari, an sanya shari’ar a matsayin laifin aikata luwadi, amma da aka fara aiwatar da sabuwar doka a jihar Jigawa, sai aka mayar da ita shari’a a matsayin na fyade a ƙarƙashin dokar hana cin zarafin mutane (VAPP) ta 2012.
“Mai laifin ya aikata laifin da ya sabawa sashe na 3 (1) (a) da (b) na dokar hana cin zarafin mutane (VAPP) da kuma hukunci a karkashin sashe na 3 (2) da 4 da 5 na dokar VAPP na shekarar 2012 na jihar Jigawa”, inji mai shari’ar.
Kotun ta kuma samu wanda ake tuhuma da laifin yin lalata da wani ƙaramin yaro ba bisa ka’ida ba, sannan ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.
