
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Majalisar Dokoki a Jihar Kano, ta bayyana goyon bayanta ga shirin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ficewa daga Jam’iyyar NNPP, tana mai kafa dalili da ƙamarin rikicin jagoranci da shari’o’i da ka iya shafar kujerun zaɓaɓɓun jami’ai.
Da yake ganawa da manema labarai a Kano ranar Laraba, jagoran mafiya rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini, ya ce cigaba da zama acikin jam’iyyar ga gwamnan abu ne mai haɗari saboda rikice-rikicen da ba a warware su ba da shari’o’in da suke barazana ga halascin jam’iyyar.
A cewarsa, rikicin cikin gida ya haifar da rashin tabbas ga halascin tsarin jagorancin NNPP da sahihancin waɗanda aka bada sunayensu a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar ga kotu.
Ya bayyana cewa, an gina matsayar majalisar ne bisa la’akari da fargabar kotuna ka iya yanke hukuncin rushe yan takarar NNPP ko da su suka ci zaɓe.
Ya yi gargaɗin faruwar irin haka ka iya sa a tsige Gwamna Abba ko kuma wasu jami’an NNPP a shari’ance.
Kazalika, ya ce mambobin majalisar na tattaunawa da gwamnan da Shugaban tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, inda ya yi kira a gare su da su yi nazari akan hikimar ɗaukar matakin domin ƙarfafa harkokin siyasarsu.
