
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Wayar da Kan Al’umma NOA, ta yi kira ga gidajen jarida da su cigaba da aiki kafaɗa-da-kafaɗa wajen inganta ayyukan wayar da kan ‘yan ƙasa.
Daraktar NOA na Jihar Oyo, Misis Ajolayo Simiat Akande ta bayyana haka a watan hira da gidan rediyon IBR FM a Ibadan, ranar Laraba.
Daraktar, wadda mataimakin harkokin labarai na hukumar a jihar, Alhaji Isiaka Kehinde ya wakilta, ta ce akwai buƙatar kafafen watsa labarai su haɓaka ƙoƙarinsu na yaɗa sahihan labarai domin daƙile ayyukan yaɗa labaran bogi da waɗanda aka jirkita ma’anoninsu.
A cewarsa, ire-iren waɗannan labaran kan ruɗar da jama’a sakamakon rushe haƙiƙanin abin da saƙonninsu suka ƙunsa, waɗanda ka iya zama barazana ga ɗaukar matsaya da haɗin kan al’umma.
Ya bayyana cewa, a ƙoƙarinta na magance matsalolin, NOA ta ƙaddamar da shirye-shiryen gidajen rediyo da talabijin musamman waɗanda suka shafi tattaunawa da jama’a kai tsaye domin tabbatar dukkan labarai ko shirye-shirye sun isa ga jama’a a yadda suke, wanda hakan zai taimaka wajen rage yaɗuwar labaran bogi acikin ‘yan ƙasa.
Ya ƙara da cewa, NOA ta samar da sama da shirye-shirye guda 78 na yarukan gida da ake yaɗawa a gidajen rediyo 198 da wasu manhajoji domin isa da saƙonninsu ga sauran al’umma.
