An sauya wa Ranar ’Yan Mazan Jiya suna a hukumance

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ayyana 15 ga watan Junairun kowace shekara a matsayin Ranar Tunawa da ‘Yan Mazan jiya a hukumance.

Ranar an ware ta ne musamman domin karrama jami’an rundunar sojojin Nijeriya da ke aiki a yanzu da kuma jinjina wa ƙoƙarin waɗanda suka rasa rayukansu a bakin aiki.

A cewar sanarwar da Daraktan yaɗa labarai na hedikwatar tsaro, Manjo Janar Samaila Uba ya fitar, ya ce za a riƙa bikin zagayowar ranar ne a ko’ina a faɗin Nijeriya ta hanyar yin shirye-shirye na tsawon mako guda waɗanda daga ciki akawai faretin jami’ai da sauransu.

Sanarwar ta ƙasa da cewa an kuma samu sauyin sunan ranar daga “Armed Forces Remembrance Day’ zuwa ‘Armed Forces Celebration and Remembrance Day’ domin dace da ainihin ma’ana abin da ake yi a taron.

Hedikwatar Tsaro ta kuma roƙi ‘yan jarida da su kiyaye amfani da sabon sunan yayin kowane rahoto akan dukkan abin da ya shafi ranar.

A ƙarshe, ta bayyana farin cikinta ga gidajen jarida bisa ƙoƙarinsu wajen lamuran tsaron ƙasa musamman a gudumawarsu na yaƙi da rashin tsaro a da ke addabar sassan ƙasar.

By Babaji