
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Jihar Jigawa ta dakatar tare da sallamar ‘yan kwangilar dafa abincin makaranta bisa zargin su da badaƙala da samar da abinci marasa inganci ga ‘yan makarantun kwana a faɗin jihar.
Hakan na zuwa ne sakamakon ƙorafe-ƙorafe daga iyaye da jama’ar gari da kuma sanya ido da jami’an Ma’aikatar Harkokin Jin ƙai da Ayuba na musamman a makarantun da ke Ƙaramar Hukumar Dutse, wato Babbar Birnin jihar.
A wata hira da manema labarai a ranar Alhamis, Kwamishinan ma’aikatar, Auwal Sankara ya ce ziyarar sanya idon na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na tabbatar da ayyukan da suka shafi walwalar ɗalibai, musamman bangaren ciyarwa sun gudana bisa tsari.
A cewarsa, a makarantar firamare ta kwana da ke Ringim, an kama wani ɗan kwangila mai suna Malam Saleh Muhammad da laifin bada shinkafa mai dingushe da kuma saɓa wa ka’idojin da gwamnati ta shimfiɗa, lamarin da ya sa aka sallame shi nan take.
Sauran waɗanda aka sallama sun haɗa da Kamalu Sulaiman, Alhaji Abdullahi Abanderi da Alhaji Umaru Chamo, waɗanda aka dakatarcda su kan samar da abincin da adadinsa bai cika ba ga makarantar Arabic and Islamic Studies, Dutse.
Duk da haka, gwamnatin jihar ta ce ƙofarta a buɗe take ga duk wata sahihiyar ƙorafi da za a gabatar ta hanyar doka.
Kwamishinan ya jaddada cewa gwamnatin Jihar Jigawa ba za ta lamunci duk wani sakaci da zai shafi walwalar ɗalibai ba, yana mai cewa an ɗauki matakin ne domin kare lafiyar yara da ingancin ilimi a makarantun faɗin jihar.
