
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote ya yi ƙorafin tsohon Shugaban Hukumar Kula da lamuran sarrafa, tacewa da sufurin fetur ta Nijeriya (NMDPR), Farouk Ahmed, gaban Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati, EFCC.
Tawagar yaɗa labaran rukunin kamfanonin ta fitar da haka a wata sanarwa yau Juma’a, inda a ciki ta ce shugaban kamfanin ya shigar da ƙarar Farouk a hedikwatar hukumar da ke Abuja.
A baya Ɗangote ya shigar da ƙarar Forouk gaban hukumar ICPC mai yaƙi da almundahana a Najeriya, domin bincikarsa kan zargin kashe dala miliyan biyar wajen karatun sakandaren ƴaƴansa a ƙasar Switzerland.
Wani abu da ake ganin ya sa Shugaban ƙasar Bola Tinubu sauke shi daga muƙamain nasa.
Saidai, a kwanakin da suka gabata ne Ɗangote ya janye ƙorafin nasa daga hukumar ICPC, kodayake hukumar ta ce za ta cigaba da binciken akan al’amarin.
Sanarwar Ɗangoten ta ce ta janye ƙorafin daga ICPC ne domin samun damar shigar da sabon ƙorafi gaban hukumar EFCC.
A ƙorafin nasa, Dangote ya buƙaci EFCC ta binciki Farouk bisa zargin tafka almundana da amfani da ofis ba bisa ƙa’ida ba, tare da gurfanar da shi a gaban kotu idan aka same shi da laifi, kamar yadda lauyansa Dakta O.J. Onoja (SAN) ya shaida a sanarwar.
