Za mu yi tankaɗe da rairaya a shugabanci domin gyara KASSOSA a zaɓe mai zuwa — Walin Gafasa

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Daya daga cikin matasan ƙungiyar Kano State Science Schools Old Students Association (KASSOSA), Kwamared Awaisu Nasir Walin Gafasa, ya bayyana cewa akwai buƙatar sake fasalin shugabancin ƙungiyar domin tabbatar da ingantaccen shugabanci a zaɓe mai zuwa.

Walin Gafasa ya yaba wa shugabancin ƙungiyar ƙarƙashin Alhaji Balarabe Nuhu Jallah bisa irin ci gaban da suka samar wa KASSOSA a matakin ƙasa, yana mai cewa mafi yawan masu muƙami a ƙungiyar sun nuna nagarta da kyakkyawar mu’amala.

Sai dai ya ce akwai wasu kaɗan da ba su tafiya da tsarin shugabanci na gaskiya da adalci, abin da ya sa matasa suka yanke shawarar tashi tsaye domin gyara al’amura ta hanyar zaɓe na gaskiya da adalci.

Ya ce matasan ƙungiyar sun gamsu da kusan kashi 99 cikin 100 na shugabannin ƙasa, amma hakan ba zai hana su tankade duk wanda ba su gamsu da salon jagorancinsa ba, domin tabbatar da muradun ƙungiyar da ci gabanta na dogon lokaci.

Taron KASSOSA na ƙasa na shekarar 2025 ya samu halartar manyan ’ya’yan ƙungiyar, ciki har da Farfesa Fatima Sulaiman Koki, wadda ta yaba wa shugabancin Jallah kan jajircewarsa wajen koyar da sana’o’i da bunƙasa ƙwarewar matasa.

Ita ma Dakta Halima Adamu Dal, wadda ta wakilci ƙaramar Ministan Abuja, Dakta Mariya Bunkure, ta ce mata na taka muhimmiyar rawa a KASSOSA, inda suke riƙe da muƙamai daban-daban, duk da cewa shugabancin ƙasa bai faɗa hannunsu ba.

A ƙarshe, shugabancin ƙungiyar na ƙasa ya yabawa manyan baƙi da suka halarci taron, ciki har da mataimakin shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Haruna Musa, shugaban hukumar kula da magunguna ta Kano, Pharm. Ghali Sule, da sauran mambobin ƙungiyar bisa gudunmawa, shawarwari da haɗin kai da suke bai wa KASSOSA a kowane lokaci.

By ukarofi