Farashin mai ya sauka sakamakon rikicin shugabanci a Venezuela

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Farashin man fetur ya soma raguwa a farkon ranar Litinin, biyo bayan rashin tabbas da ya mamaye kasuwa kan buƙatar samar da mai, bayan da Amurka ta kwace ikon shugabancin gwamnatin ƙasar ɓenezuela tare da tashe-tashen hankula na siyasa a tsakanin mambobin ƙasashe masu samar da man fetur na OPEC.

Masu nazarin kasuwa na duba yiwuwar tasirin matakin sojan Amurka a ɓenezuela, a daidai lokacin da ake fama da yawan man da ke kasuwa a duniya da kuma raunin ƙaruwar buƙata.

Man Brent ya kasance a kan dalar Amurka 60.33 kowacce ganga, wanda ke nuna faɗuwar kaso 0.6 idan aka kwatanta da kasuwar ranar Juma’a a dalar 60.73.

Haka zalika, man Amurka, West Teɗas Intermediate (WTI), ya tsaya a dalar 56.82 kowace ganga, ya ragu da kusan kaso 0.7 idan aka kwatanta da dalar 57.21 na makon da ya gabata. Farashin ya buɗe da ƙasa a kasuwannin Asiya, ya ɗan farfaɗo na ɗan lokaci, amma ya sake komawa ƙasa saboda yawaitar man da ke kasuwa, duk da ƙaruwar damuwa kan yanayin siyasa a duniya.

A ranar Asabar, Amurka ta sanar da kama Shugaban Venezuela, Nicolas Maduro, inda Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Washington za ta karɓi ikon ƙasar har sai an samu damar miƙa mulki ga wata sabuwar gwamnati, ba tare da bayyana yadda hakan zai tabbata ba.

ɓenezuela na da mafi girman ajiyar man fetur a duniya, har ta zarce Saudiyya wadda ke jagorantar OPEC, sai dai samar da man ƙasar ya fazi matuƙa sakamakon shekaru na rashin kyakkyawan shugabanci da kuma takunkuman tattalin arziki.

“Amurka ce ke da iko a ɓenezuela a yanzu,” inji Trump, bayan wani aikin soji da ya kai ga kama Maduro da matarsa, tare da kai su Amurka domin fuskantar tuhume-tuhumen laifi.

“Mu na hulɗa da mutanen da aka riga aka rantsar. Kada ku tambaye ni wa ke da iko, domin amsar da zan bayar za ta tayar da ce-ce-ku-ce,” inji Trump yayin da yake magana da manema labarai a cikin jirgin Air Force One, bayan an tambaye shi ko ya tuntuɓi Mataimakiyar Shugaban ƙasa Delcy Rodriguez, wadda babbar kotun Venezuela ta naɗa a matsayin riƙon shugabanci.

Trump ya ce, abin da Amurka ke buƙata shi ne samun cikakken damar shiga, musamman dangane da man fetur da sauran albarkatun da za su ba da damar sake gina ƙasar.

Masana harkar makamashi na cewa har yanzu wadatar man fetur a duniya na nan daram, lamarin da ke rage yiwuwar tashin farashi cikin gajeren lokaci, ko da kuwa fitar man ɓenezuela ta ƙara raguwa.

Rahotanni sun nuna cewa harin sojan Amurka bai lalata cibiyoyin haƙo man fetur ko matatun mai na Venezuela ba. Trump ya kuma yi gargaɗin cewa za a iya sake ƙaddamar da wani aikin soji na biyu idan jami’an da suka rage a gwamnatin Venezuela suka ƙi bayar da haɗin kai.

By ukarofi