Daga DAUDA USMAN a Legas
Makarantar Madarasatul Darul ƙur’anil Karim, wadda ke unguwar Mile 12 a Jihar Legas, ta gudanar da bikin walimar yaye ɗalibai hamsin da biyu karo na biyar a ranar Lahadin da ta gabata, a wani biki da ya samu halartar manyan malamai, shugabannin addini da al’ummar unguwar baki ɗaya.
Makarantar, wadda ke lamba 17 layin Oliyori, unguwar Mile 12, kuma ta ke ƙarƙashin jagorancin Shugaban Makaranta, Sheikh Malam Gambo Funtuwa, ɗan asalin Jihar Katsina, ta gudanar da taron ne a harabar Makarantar Maidon Primary School da ke layin gidan Sarkin Hausawan Mile 12. Sheikh Gambo Funtuwa shi ne Babban Limamin Masallacin Juma’a da ke ƙofar fadar Sarkin Hausawan Mile 12.
Bikin walimar ya samu halartar malamai daga ƙungiyoyi da dariku daban-daban na Musulunci, ciki har da ƙungiyar Izala, Darikar Tijjaniyya da Shi’a, tare da shugabannin makarantun Islamiyya da sauran manyan al’ummar unguwar Mile 12.
Daga cikin manyan malamai da suka halarci taron akwai Sheikh Malam Abdullahi Jos na ƙungiyar Izala, Sheikh Malam Idris Al-Salafi Mile 12, Babban Ladamin Masallacin Juma’a na Izala Mile 12, Malam Rabi’u Babban Limamin Masallacin Juma’a na ’Yan Shinkafa Mile 12, da Sheikh Malam Usman Umar, wakilin mabiya mazhabar Shi’a a Mile 12, tare da wasu malamai da dama.
Haka kuma, taron ya samu halartar manyan baki na musamman, ciki har da Alhaji Ibrahim ɗan Soja, Sarkin ’Yan Gwagena na jihohi goma sha bakwai, wanda ya samu wakilcin sakatarensa Alhaji Salisu Lale Gidan Kwali, Ojota. Sauran manyan baki sun haɗa da Alhaji Zubairu Abduljalalu, Shugaban Al’ummar Nijar mazauna Mile 12, Mai Martaba Sarkin Zabarmawan Mile 12, Alhaji Isiyaku, da kuma uban taron, Mai Martaba Sarkin Hausawan Mile 12, Alhaji Haruna Jibirilu.
Tun daga buɗe taron da addu’a, malamai mahalarta suka ci gaba da gabatar da wa’azi, inda suka jaddada muhimmancin sanya yara a makarantun koyar da karatun addinin Musulunci, tare da jan hankalin iyaye kan rawar da suke takawa wajen tarbiyyar ’ya’yansu.
Daga bisani, ɗaliban da aka yaye, maza da mata, suka karanta ayoyin Alkur’ani Mai Tsarki, kowa gwargwadon abin da ya sauƙaƙa masa. A ƙarshen taron, kwamitin malaman makarantar suka raba wa ɗaliban da aka yaye takardun shaidar kammala karatunsu.
A nasa jawabin, Shugaban Makarantar, Sheikh Malam Gambo Funtuwa, ya gode wa iyayen ɗalibai bisa haɗin kai da goyon bayan da suke bai wa makarantar, musamman wajen tura ’ya’yansu makaranta a kan lokaci, yana mai cewa hakan na taimakawa yara wajen fahimtar karatu cikin kankanin lokaci. Ya kuma yaba wa malaman makarantar bisa jajircewa da kaifin basira da suke amfani da su wajen koyar da ɗalibai.
A ƙarshe, ya yi wa dukkan mahalarta taron fatan alheri tare da addu’ar Allah Ya mayar da su gidajensu lafiya.
