’Yan kasuwar Bichi sun yi kira kan gina ƙananan masana’antu don farfaɗo da tattalin arziki

Spread the love

Daga WAKILINMU

An shawarci ’yan kasuwar Zamani ta ƙaramar Hukumar Bichi da su ƙara haɗa kai tare da neman shawarwarin masana domin kafa kananan masana’antu da bunƙasa noman rani, a matsayin hanya ta ƙarfafa tattalin arzikin yankin.

Wannan kira ya fito ne daga tsohon Shugaban Jami’an Tsaron Farin Kaya na Kasa, Alhaji Yusuf Magaji Bichi, a yayin da ƙungiyar ’yan kasuwar Zamani ta Bichi ta kai masa ziyarar girmamawa a gidansa da ke cikin garin Bichi.

Da yake jawabi yayin taron, Alhaji Yusuf Magaji ya bayyana matuƙar jin daɗinsa kan wannan ziyara, yana mai bayyana haɗin kan da ke tsakanin ’yan kasuwar a matsayin ginshiƙin samun nasara da ci gaban kowace ƙungiya. Ya jaddada muhimmancin yin aiki tare domin cimma muradun da aka sanya a gaba.

Tsohon jami’in tsaron ya kuma yi alƙawarin ci gaba da ba da gudunmawa da goyon baya ga duk wani shiri da ƙungiyar za ta bullo da shi, musamman waɗanda ke da nasaba da bunƙasa kasuwanci, samar da ayyukan yi da kuma tabbatar da tsaro. Daga bisani, ya yi wa ’yan kasuwar fatan alheri da samun cigaba mai ɗorewa.

Tun da fari, Shugaban ƙungiyar ’yan kasuwar Zamani ta Bichi, Alhaji Abubakar Mazahim Saleh, ya bayyana jin daɗin ƙungiyar kan kyakkyawar tarbar da suka samu. Ya bayyana ziyarar a matsayin wata dama ta neman shawarwari masu amfani, musamman a kan harkokin kasuwanci da batutuwan tsaro a ƙaramar Hukumar Bichi da kuma Arewa ta Kano gaba ɗaya.

Kazalika, ’yan kasuwar sun bayyana Alhaji Yusuf Magaji Bichi a matsayin shugaba abin koyi, wanda tarihin Bichi ba zai manta da irin gagarumar gudunmawar da ya bayar ba, musamman wajen taimakawa matasa samun ayyukan yi a fannoni daban-daban.

A wani ɓangare na labarin, ƙungiyar ’yan kasuwar ta yaba wa Mai Ba Gwamna Shawara kan Tsaftar Muhalli, Injiniya Abdullahi Shehu Bichi, bisa aikin feshin maganin sauro da aka gudanar a kasuwar Zamani da kuma babban asibitin Bichi, wanda suka ce ya taimaka wajen kare lafiyar al’umma.

By ukarofi