Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) ta bayyana cewa kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) sun samu kuɗin shiga na Naira biliyan N570.25 daga cikin biliyan N706.61 da suka caji kwastomomi a ƙarshen shekarar 2025.
Wannan, a cewar rahoton hukumar, na nuna ingancin tara kuɗi kashi 80.70 cikin 100, lamarin da ke nuna ƙarin kashi 4.63 idan aka kwatanta da tsakiyar shekarar, wanda ya tsaya a kashi 76.07 cikin 100.
Rahoton ƙarshen shekarar 2025 da NERC ta fitar a ranar Talata ya nuna cewa duk da samun wannan kuɗin shiga, DisCos sun biya kuɗi biliyan N400.48 a matsayin basussukan da ake bin su a sama, inda suka saka biliyan N381.29, suka bar bashin biliyab N19.18.
Wannan ya nuna cewa matakin biyan basussuka ya kai kashi 95.21 cikin 100, kaɗan ƙasa da kashi 95.65 da aka samu a tsakiyar shekarar.
NERC ta kuma ce jimillar kuɗin wutar lantarki da DisCos suka karɓa daga kamfanonin samar da wuta a ƙarshen shekarar 2025 ya kai biliyan N854.53, yayin da aka caji kwastomomi biliyan N706.61.
Wannan ya nuna ingancin caji (billing efficiency) na kashi 82.69 cikin 100, ƙarin kashi 1.08 idan aka kwatanta da tsakiyar 2025. Duk da haka, rahoton ya nuna cewa DisCos sun yi asarar kucin caji har biliyan N147.92 a wannan lokaci.
A ɓangaren asarar fasaha, kasuwanci da tara kuɗi (ATC&C), NERC ta ce matsakaicin asara ya kai kashi 33.27 cikin 100 a dukkan DisCos, abin da ya wuce burin tsarin MYTO na kashi 20.54 cikin 100 da tazarar kashi 12.73. Wannan ya haifar da asarar kuɗaɗen shiga da ta kai kusan N108.753 biliyan. Duk da samun ɗan ragi idan aka kwatanta da tsakitar shekarar, rahoton ya nuna cewa dukkan DisCos – in banda Eko da Ikeja – sun kasa cimma burin ATC&C, inda Kaduna DisCo ta fi kowa tara kuɗi.
A ɓangaren saka mitoci, an sanya mitoci 228,614 a ƙarshen 2025, ƙarin kashi 0.73 idan aka kwatanta da tsakiyar shekarar. Yawancin mitocin an sanya su ne ƙarƙashin shirin MAP, sai wasu ta hannun masu saka jari da kuma shirin DISREP.
Rahoton ya kuma bayyana cewa matsakaicin samar da wutar lantarki a kowace sa’a a ƙarshen shekarar ya kai 4,179.15MWh/h, wanda ya ƙaru zuwa jimillar 9,227.56GWh. Wannan ya nuna raguwa idan aka kwatanta da tsakiyar shekarar abin da NERC ta alaƙanta da raguwar karɓar wuta daga abokan hulɗa.
A ɓangaren aikin turakun lantarki, an samu hatsarin rushewar tsarin wuta sau ɗaya kacal a ƙarshen 2025, inda aka samu cikakken faɗuwarsa a ranar 10 ga Satumba, 2025. Game da ƙorafe-ƙorafen kwastomomi, DisCos sun warware ƙorafe-ƙorafe 519 daga cikin 833 da aka kai NERC-CCU, yayin da jimillar ƙorafe-ƙorafen da aka karɓa ta ragu da kashi 26.06 idan aka kwatanta da tsakiyar shekarar. NERC ta ce matsalolin da aka fi yawan ƙorafi a kansu su ne mita, caji da katsewar wuta.
