
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai wani mummunan hari akan ayarin masu bikin aure a Unguwar Nagunda da ke ƙaramar hukumar Ƙanƙara a jihar Katsina, inda suka kashe mutune guda biyu.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kuma raunata wasu da dama ciki har da amarya.
Al’amarin ya faru ne a daren Lahadi, inda ‘yan bindigar suka buɗe wuta a yayin da ayarin bikin ke wucewa, lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici.
Haka kuma, an sace wasu baƙi dai har yanzu ba a tantance adadinsu ba yayin farmakin.
Wani jami’in tsaro ya bayyana cewa har zuwa safiyar Litinin, iyalan mutanen da abin ya shafa na cigaba da neman tabbacin adadin waɗanda aka sace.
Ƙoƙarin jin ta bakin Kakakin Rundunar yansandan jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiq ya ci tura a yayin haɗa wannan rahoto kasancewar bai amsa kira ko saƙonnin da aka aike masa ba.
Wannan al’amari na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnatin jihar ke shirin sako wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne su guda 70 daga komar hukuma bisa sharuɗɗan zaman sulhu tsakanin yankunan da ayyukan ta’addanci ya shafa da tubabbun ‘yan bindiga a jihar.
Gwamnatin jihar ta hannun ma’aikatar shari’arta ce shirin ƙulla yarjejeniyar sulhu ya yi sanadin sako aƙalla mutane guda 1,000 da aka yi garkuwa da su a hare-hare mabambanta.
