Gwamnatin katsina za ta saki ‘yan bindiga 70 da ke tsare a gidan yari

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnatin jihar ta ce za ta saki ɓarayin daji 70 dake tsare a gidan yarin jihar, sai dai gwamnatin ta bayyana cewa yunƙurin sakin ‘yan bindigar mataki ne ƙoƙarin ɗorewar yarjejeniyar zaman lafiya da ake yi da dabobin ‘yan bindigar da ke addabar sassan jihar, musamman a yankunan ƙaramar hukumar Ƙanƙara.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Nasir Muazu ne ya yi bayani game da yarjejeniyar da aka cimma da ƙoƙarin gwamnati na kiyaye hakan, Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Ya kuma ce za a saki ‘yan bindigar ne domin ƙarfafa yarjejeniyar sulhu da aka cimma tsakanin garuruwan da abin ya shafa da kuma ’yan ta’addar da suka tuba a ƙananan hukumomi 15 na jihar.

A cewarsa, wannan yarjejeniyar ta riga ta samar da sakamako mai kyau, inda aka samu nasarar sakin kimanin mutane 1,000 da aka yi garkuwa da su a baya ba tare da biyan kuɗin fansa ba.

Sai dai wannan mataki na yunƙurin sakin ɓarayin dajin ya haifar da zazzafar muhawara a kafafen sadarwar zamani.

By ukarofi