Manchester United ta naɗa Michael Carrick a matsayin kocin riƙo

Spread the love

A yau Talata ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta tabbatar da tsohon ɗan wasanta, Michael Carrick a matsayin sabon manajan riƙo har zuwa ƙarshen kakar 2025/26.

Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan da korar Rúben Amorim a makon da ya gabata, da kuma gajeren lokacin da Darren Fletcher ya yi.

Ana ganin Carrick ya dawo tsohuwar ƙungiyar tasa ne don ceto ta daga halin da take ciki.

Masu Taimaka Masa sun haɗa da Steve Holland, tsohon mataimakin kocin Ingila; Jonathan Woodgate, abokin aikin Carrick daga Middlesbrough; sai kuma Jonny Evans, wanda zai cigaba da taimaka wa fannin horarwa.

A yanzu haka dai, wasan farko da Carrick zai jagoranta shine wanda ƙungiyar za ta yi da maƙociyarta, wato Manchester City a ranar Asabar mai zuwa.

Sannan Man United a yanzu tana matsayi na 7 a teburin Premier League, kuma babban burinsa shine ganin ƙungiyar ta koma sahun manya hudu, wato ‘top 4’.

By Babaji