Amurka ta aiko wa Nijeriya kayan yaƙi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewa, Amurka ta kawo wa Nijeriya kayan yaƙi domin bunƙasa ayyukan hukumomin tsaro a sassan ƙasar.

AFRICOM ta sanar da haka ta kafar X a yau Talata, inda ta ce tuni dakarun Amurka suka kai wa hukumomin Nijeriya kayan a Birnin Tarayya Abuja.

Hakan wani ɓangare ne na tallafa wa ƙoƙarin Nijeriya wajen sauke ayyukanta na fannin tsaro da kuma ƙarfafa alaƙar tsaro da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Gwamnatin Tarayya ta ce, gwamnatin Amurka ta jaddada ƙudirinta na ƙarfafa haɗin-gwiwar tsaro da Nijeriya ciki har da samar da agajin ayyukan leƙen asiri, kayan yaƙi da wasu ababen da fannin tsaro ke buƙata na ƙarfafa atisayen yaƙi da ta’addanci a Nijeriya.

A watan Nuwamba ne Nijeriya ta aike da wata tawaga zuwa Washington DC da nufin ƙarfafa alaƙar tsaro a tsakaninsu da faɗaɗa fagagen haɗin-gwiwa.

A cewar Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga, ƙasashen sun cimma matsaya da yarjejeniyoyi akan haɗin-gwiwa don tabbatar da salo ɗaya na bin ababen da aka yarje akansu.

Ya ƙara da cewa, tawagar ta jaddada ƙoƙarin gwamnati na inganta matakan bada kariya ga fararen hula a sassan ƙasar.

By Babaji