Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Waɗanda aka rantsar sun haɗa da Tukur Hassan Ɗan Ali shugaban ƙungiyar ‘yan Jarida reshen jihar Katsina daga ƙaramar hukumar Ɗanmusa da Junaidu Muntari daga ƙaramar hukumar Kankara sai Yahaya Abdullahi daga ƙaramar hukumar Safana.
Haka zalika, Gwamna Raɗɗa ya rantsar da Alhaji Lawal Mukhtar Ɓaure a matsayin mai ba da shawara na musamman (Special Adviser).
Da yake jawabi bayan rantsuwar, gwamnan ya yi kira ga sabbin masu muƙaman da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, amana da nuna kishin jiha da ƙasa baki ɗaya.
Dikko ya jaddada cewa gwamnatinsa na da burin inganta tsarin gudanarwa da samar da hidimomi masu inganci ga al’umma.
Bikin rantsuwar ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, ‘yan uwa da abokan arziki na waɗanda aka rantsar, tare da sauran mutane.
