Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wata uwa mai ’ya’ya biyar, Aishatu Umar, ta rasu a jihar Kano sakamakon abin da iyalanta ke zargi a matsayin sakacin likitoci a asibitin Abubakar Imam Urology Centre dake Kano, inda aka ce an bar mata almakashin aikin tiyata a cikin jikinta bayan an yi mata aiki a watan Satumba.
Rasuwarta ta zo ne ƙasa da mako guda bayan rahoton mutuwar wani yaro ɗan marubuciya Chimamanda Adichie, wanda aka ce ya faru sakamakon sakaci a bangaren kiwon lafiya, lamarin da ya ƙara hura wutar fushi da kira ga ɗaukar mataki kan ingancin tsarin kiwon lafiya a ƙasar.
Rahotanni sun ce Aishatu ta rasu da misalin ƙarfe 1:00 na dare a ranar Talata, bayan shafe watanni tana fama da matsanancin ciwon ciki bayan an yi mata tiyata, wadda a farko aka ce za ta taimaka wajen inganta lafiyarta. Maimakon haka, halin nata ya ta’azzara, har ya kai ga mutuwarta.
Yayin da yake magana a madadin iyalan marigayiyar, Abubakar Mohammed ya ce Aishatu ta kamu da rashin lafiya ne watanni da suka gabata, inda aka kwantar da ita a cibiyar urology domin yi mata tiyata. Ya bayyana cewa bayan kammala aikin, matsaloli suka biyo baya, inda ta fara fama da ciwon ciki mai tsanani da ke dawowa akai-akai.
A cewarsa, marigayiyar ta riƙa komawa asibitin tsawon kusan watanni huɗu tana ƙorafin halin da take ciki, amma iyalan sun zargi ma’aikatan lafiya da ba ta magungunan rage raɗaɗi kawai ba tare da yin cikakken bincike don gano musabbabin matsalar ba.
Iyalan sun ƙara da cewa kwanaki biyu kacal kafin rasuwarta ne aka yi mata cikakken gwaji, ciki har da hotunan na’ura, inda aka gano cewa an bar almakashi na tiyata a cikin jikinta tun lokacin aikin da aka yi mata a watan Satumba.
Bayan wannan ganowa, an ce ana shirin sake yi mata wani aikin gyara, amma halin nata ya ƙara tsananta cikin gaggawa kafin a kai ga yi mata aikin, lamarin da ya kai ga mutuwarta.
Iyalan sun bayyana wannan lamari a matsayin mummunan tauye ƙa’idojin aikin likitanci da tsaron marasa lafiya, tare da kiran gwamnatin jihar Kano da hukumomin da ke kula da harkokin lafiya da su gudanar da bincike mai zurfi domin tabbatar da an yi adalci.
Yayin da take mayar da martani, mai magana da yawun Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano, Samira Suleiman, ta ce hukumar ta samu rahoton lamarin kuma ta miƙa ta’aziyya ga iyalan marigayiyar.
A cikin wata sanarwa, ta ce babban sakataren hukumar, Dakta Mansur Mudi Nagoda, ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa da gaskiya kan zargin, yana mai tabbatar da cewa za a ɗauki matakin da ya dace idan an tabbatar da sakaci.
Gwamnatin Kano ta dakatar da ma’aikata uku:
Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano ta tabbatar da cewa lamarin mutuwar Aishatu Umar ya faru ne a cibiyar Abubakar Imam Urology Centre, bayan zargin sakacin likitoci da ya janyo cece-kuce a faɗin jihar.
A cikin wata sanarwa da jami’ar hulɗa da jama’a ta hukumar, Samira Suleiman, ta fitar a daren Talata, hukumar ta ce binciken farko da babban sakatarenta, Dakta Mansur Mudi Nagoda, ya bayar da umarni, ya tabbatar da cewa “lamarin baƙin ciki da ya shafi marigayiya Aishatu Umar ya faru a cibiyar Abubakar Imam Urology Centre.”
Sanarwar ta ce, bisa ƙudirin hukumar na tabbatar da ɗaukar alhaki, “an dakatar da ma’aikata uku da ke da hannu kai tsaye a lamarin daga duk wani aikin jinya nan take.”
Hukumar ta ƙara da cewa, an miƙa lamarin ga Kwamitin ƙa’idojin ɗabi’a na Likitoci na Jihar Kano domin ci gaba da bincike da ɗaukar matakin ladabtarwa idan ya dace.
A cewar hukumar, hakan zai tabbatar da “ɗaukar matakin ladabtarwa da ya dace bisa dokoki, ƙa’idoji da kuma ɗabi’a.”
