Bankuna sun fara cire harajin VAT kan tura kuɗi ta tsarin USSD

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta umarci dukkan bankuna da kamfanonin fasahar kuɗi, wato ‘Fintech’ da ke aiki a Nijeriya da su fara karɓar harajin kashi 7.5 cikin 100 na VAT kan wasu ayyukan banki ta lantarki, daga ranar Litinin 19 ga Janairu, 2026.

Rahotanni sun nuna cewa an sanar da kwastomomi wannan sabon mataki ta hanyar saƙonnin imel da wasu bankuna suka aike, ciki har da Moniepoint. A cikin sanarwar, an jaddada cewa harajin VAT zai shafi kuɗin ayyuka ne kawai, ba kuɗin da ake aikawa ba.

Misali, idan banki ya caji N100 a matsayin kuɗin sabis na tura kuɗi, kashi 7.5 na VAT zai lissafta ne a kan N100 ɗin, ba a kan adadin kuɗin da ake aikawa ba. Sabis da abin ya shafa sun haɗa da cajin tura kuzi ta wayar hannu, kuɗin mu’amala ta USSD, da kuma kuɗin fitar da katin ATM.

A cewar Moniepoint, “Daga ranar Litinin 19 ga Janairu, 2026, doka ta wajabta mana karɓar kashi 7.5 na VAT domin miƙa wa Hukumar Haraji ta Nijeriya, wato Nigerian Revenue Service.” Kamfanin ya ƙara da cewa, “Harajin zai shafi wasu sabis ɗin banki na lantarki kamar cajin tura kuɗi, kuɗin USSD da na katin ATM.”

Ana sa ran sauran bankuna da kamfanonin fintech za su fitar da irin wannan sanarwa yayin da ranar fara aiki da sabon tsarin ke ƙaratowa. 

Hukumar Haraji ta Nijeriya (NRS), wadda ta maye gurbin tsohuwar FIRS, ta kafa wannan mataki ne domin tabbatar da cewa dukkan bankuna da masu bayar da kula da ayyukan kuɗi suna bin doka wajen karɓa da miƙa harajin VAT.

Moniepoint ta bayyana cewa wannan ba ƙarin kuɗi ba ne daga ɓangaren masu bayar da sabis, illa cika umarnin gwamnati. “Ba mu ƙara kuɗin sabis ba, doka ce ta wajabta mana karɓa da miƙa VAT,” inji kamfanin.

Gwamnati ta ce matakin na daga cikin yunƙurinta na daidaita karɓar haraji a ɓangaren sabis na kuɗi na zamani tare da ƙara hanyoyin samun kuɗaɗen shiga, musamman ganin yadda tattalin arzikin dijital ke ƙara bunƙasa a ƙasar.

Ko da yake an daɗe ana da tanadin haraji kan wasu sabis na banki, amma yanzu NRS ta fara aiwatar da cikakken bin doka a dukkan dandamali domin rufe giɓi da kuma kawo daidaito a tsarin.

An kuma tabbatar wa kwastomomi cewa za a riƙa bayyana adadin VAT a sarari a kan rasit, bayanan asusu da rahotannin mu’amalar kuɗi. Sai dai wasu sabis kamar ribar da ake samu daga ajiyar kuɗi a banki ba za su kasance ƙarƙashin VAT ba.

Wannan sabon umarni ya biyo bayan sanarwar da wasu bankuna suka fitar a watan Disamba, inda suka fara cire kuɗin stamp na N50 kan duk wata mu’amalar lantarki da ta kai N10,000 zuwa sama, bisa tanadin sabuwar dokar haraji.

By ukarofi