Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD
Jam’iyyar ADP ta miƙa saƙon taya murna da gaisuwa ga Rundunar Sojojin Nijeriya yayin bikin Ranar Tunawa da Rundunar Soji, wadda ake gudanarwa domin girmama jarumtaka, sadaukarwa da hidimar ƙasa da dakarun Nijeriya ke yi ba tare da gajiyawa ba.
A cikin wata sanarwa da shugaban jam’iyyar, Injiniya Yabagi Yusuf Sani, ya sanya wa hannu, ADP ta ce wannan rana ta musamman na nuni da muhimmancin girmama jaruman da suka sadaukar da rayukansu wajen kare haɗin kan ƙasa, ikon Nijeriya da kuma tsarin mulkin dimokuraɗiyya.
Jam’iyyar ta bayyana cewa sadaukarwar waɗannan jarumai ita ce ginshiƙin ’yanci da ‘yan Nijeriya ke morewa a yau, tare da zama darasi na har abada kan kishin ƙasa da biyayya ga aiki.
ADP ta kuma yaba wa dakarun da ke kan aiki a halin yanzu, wazanda ke ci gaba da fuskantar ƙalubale masu tsanani wajen yaƙi da ta’addanci, ‘yan bindiga, sace-sacen mutane da sauran barazanar tsaro a faɗin ƙasar nan.
Jam’iyyar ta ce rundunar soji ta ɗauki nauyi mai girma a ‘yan shekarun nan, inda take gudanar da ayyuka a fannoni daban-daban na tsaro tare da daidaita dabaru da sabbin nau’o’in barazana.
Sanarwar ta jaddada cewa juriya da ƙwarewar dakarun sun cancanci yabo da godiya daga dukkan ‘yan Nijeriya. Sai dai ADP ta bayyana cewa matsalolin rashin tsaro da ake fuskanta a ƙasar nan ba laifin rundunar soji ba ne, illa sakamakon giɓin shugabanci, matsalolin tattalin arziki, sauyin yanayi da kuma yankunan da gwamnati ba ta da cikakken iko a kansu.
Jam’iyyar ta yi kira da a daidaita sadaukarwar dakarun da ingantattun dabarun tsaro na zamani da ke dogaro da bayanan sirri, da kuma tabbatar da walwala da kulawa ga jami’an tsaro bisa doka da oda. Haka kuma, ta nemi a gaggauta tabbatar da tsaro bayan kammala hare-hare ta hanyar ƙarfafa aikin ‘yan sanda, shari’a da samar da hanyoyin samun abin yi ga al’umma.
ADP ta ƙara da cewa, ya zama wajibi a samar da tsarin haɗin gwiwa tsakanin dukkan sassan gwamnati domin sauya nasarorin fagen fama zuwa tabbataccen tsaro ga fararen hula.
A cewar jam’iyyar, wannan ne kaɗai zai tabbatar da cewa jinin jaruman da suka rasu bai zube a banza ba.
Yayin da ‘yan Nijeriya ke tunawa da waɗanda suka rasa rayukansu, ADP ta jaddada ƙudirin ta na goyon bayan manufofi da ke ƙarfafa tsaron ƙasa, kare rayukan fararen hula da dawo da cikakken ikon gwamnati a kowace al’umma.
Jam’iyyar ta kammala da addu’a, tana roƙon Allah Ya jiƙan jaruman da suka rasu, Ya kare masu rai, Ya ba su kariya da kima, tare da roƙon Allah Ya sanya Nijeriya ta zama ƙasa mai ƙarfi, tsaro da haɗin kai.
