Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Mai Martaba Sarkin Sharifan Gaya, Malam Nazifi Sulaiman, ya nuna rashin jin daɗinsa kan rashin halartar shugabanni da masu madafun iko wajen bikin saukar Alƙur’ani na ɗalibai 153 karo na huɗu da makarantar Ma’ahad Khairulbariyya Islamiyya ta shirya a Gaya.
Sarkin ya bayyana cewa halartar shugabanni da sarakuna a irin waɗannan taruka na ƙara wa yara ƙwarin gwiwa da farin ciki, yana mai cewa babu wuri mafi dacewa da shugabanni su halarta kamar inda ake karatun littafin Allah.
Ya nuna damuwa kan yadda yankin ke da ‘yan majalisa, shugabannin ƙananan hukumomi da sarakuna, amma babu wanda ya halarta ko turo wakili, lamarin da ya bayyana a matsayin rashin kulawa da harkokin addini.
A nasa jawabin, shugaban makarantar, Malam Muhammad Bashir Idris, ya bayyana cewa makarantar na fama da ƙarancin ajujuwa da wurin zama, tare da yin kira ga gwamnati da al’umma su tallafa. Ya kuma ja hankalin dalibai da cewa saukar Alƙur’ani ba ƙarshen karatu ba ne, illa sabon mataki na zurfafa neman ilimi.
