CPEGLD ta karrama Hajiya Rabi Inuwa bisa gudummawa a ilimi

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano 

Cibiyar wayar da kan al’umma da kyakkyawan shugabanci (CPEGLD) ta karrama Daraktar Hukumar Ilimi ta Jihar Kano, Hajiya Rabi Inuwa Hussaini, bisa jajircewarta wajen bunƙasa harkar ilimi da inganta shugabanci a hukumar.

Da yake mika lambar yabo, Daraktan cibiyar, Kwamared Auwalu Yalwa, ya ce an zabi Hajiya Rabi ne sakamakon hazakarta da sauye-sauyen da ta kawo, wanda hakan ya sanya jihar Kano ta zama abin koyi a fannin ilimi a Nijeriya.

Cibiyar ta bayyana cewa zuwanta ya kawo raguwar koke-koke musamman kan jarabawar BECE, tare da inganta tsarin aiki da rarraba nauyin aiki ga ma’aikata yadda ya dace, lamarin da ya haifar da gagarumar nasara a hukumar.

Da take jawabin godiya, Hajiya Rabi Inuwa ta ce wannan karramawa za ta ƙara mata ƙwarin gwiwar ninka ƙoƙarinta. Ta yabawa Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa goyon bayan da yake bai wa hukumar, tana mai cewa babu shakka gudummawarsa ce ta sa aka cimma nasarorin da ake gani a yau.

By ukarofi