Allah ya cusa mana ƙauna da son hidimar addini a zukatanmu – Malama Fatima Fagge

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Malama Fatima Muhammad Fagge, shugabar cibiyar Zadulhuda Foundation da ke Kano, ta bayyana cewa babu wata ni’ima da Allah Ya yi musu da ta fi abin alfahari kamar yadda Ya yi amfani da su wajen hidimar addinin Musulunci, musamman ta fuskar gyaran rayuwar aure.

Malama Fatima ta bayyana hakan ne a ranar Asabar da ta gabata yayin bikin yaye ɗalibai mata 684 da suka kammala horo na tsawon watanni uku kan zaman rayuwar aure a Musulunci, wanda aka gudanar a cibiyar da ke Fagge. Ta ce an shirya bikin ne domin cika addu’ar kammala saukar Alƙur’ani mai girma sau 12,000 da cibiyar ta yi domin neman zaman lafiya da bunƙasar arziki ga ƙasa baki ɗaya.

Ta ƙara da cewa zuwa yanzu cibiyar ta yaye ɗalibai sama da 584 da suka haɗa da ‘yan mata, zawarawa da matan aure, inda sakamakon horon ya haifar da kyakkyawan sauyi a rayuwar aurensu, lamarin da ke sa cibiyar ke samun kiraye-kirayen godiya daga wurare daban-daban.

A yayin taron, cibiyar ta karrama wasu fitattun mutane da suka bayar da gudummawa ga addini da cigaban cibiyar, ciki har da Malam Umar Sani Fagge, wanda aka karrama bisa gudummawarsa a matsayin uba, malami, mai tunatarwa da kuma jajirtaccen mai hangen nesa a harkar addini.

By ukarofi