‘Yan bindiga sun halaka malamin addini a Kaduna

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Laraba wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka halaka wani malamin addini a yankin Layin Ɗan-Auta da ke Gundumar Kuyello a Ƙaramar Hukumar Birnin-Gwarin Jihar Kaduna.

Mazauna yankin sun aike wa jaridar Premium Time hoton gawar mamacin, da aka bayyana da suna Bello Abubakar, wanda na’ibin limami ne na wani masallacin ƙungiyar Izala da ke ƙauyen.

An kai masa farmaki tare da kashe shi ne yayin da yake aikin jidar itatuwa a gundumar, wadda ke gabashin Birnin-Gwari.

Wani mazaunin yankin da ya zanta da manema labarai, ya ce ana kai wa garin Kutemeshe da ke kusa da su hari kusan kullum. Saidai ba a iya sanar da hukumomi saboda tsoron faɗawa cikin haɗari.

Ya bayyana cewa, al’amarin tsaro a yankin Layin Ɗan-Auta ya caɓe domin wasu mazauna su bakwai da aka sace har yanzu suna komar ‘yan bindiga.

Al’amarin kisan limamin ya sanya firgici acikin al’umma musamman duba da yadda ake girmama shi bisa hidimarsa ta addini da ta haɗa da karantar da ilimin Alƙur’ani mai girma da jagorantar sallolin farilla a watan Ramadana.

Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, ƙoƙarin ji ta bakin Kakakin Rundunar ‘yan sandan Kaduna, Mansir Hassan ya ci tura.

By Babaji