An kama boka a Mali bayan yi wa ’yan ƙasar alƙawarin lashe AFCON

Spread the love

Hukumomin tsaro a ƙasar Mali sun kama wani boka da ya kira kansa masani bayan ya yi alƙawarin zai taimaka wa ƙasar su lashe Gasar Kofin ƙasashen Afrika (AFCON) ta hanyar sihiri, inda ya karɓi fiye da yuro dubu talatin da uku daga jama’a.

An kama mutumin ne bayan fitar Mali daga gasar.

Rahotanni sun bayyana cewa mutumin, mai suna Sinayogo, an kama shi ne a Bamako ranar Asabar, kwana guda bayan Senegal ta doke Mali da ci 1-0 a wasan kwata fainal na AFCON 2025. 

Kafin haka, Sinayogo ya riƙa bayyana kansa a matsayin marabout, wato boka na gargajiya, yana iƙirarin cewa zai iya tabbatar wa Mali nasara ta ruhaniya a gasar.

An ce ya tara sama da kuɗin ƙasar, wato franc CFA miliyan 22 daga magoya baya da masu goyon bayan ƙungiyar, inda ya tabbatar musu cewa Mali za ta ɗauki kofin. Amma bayan shan kashi, fusatattun jama’a sun taru a gidansa suna neman ya yi musu bayani, lamarin da ya tilasta ‘yan sanda shiga tsakani domin fitar da shi daga gidan don kare lafiyarsa.

Daga bisani aka kai shi sashen yaƙi da laifukan yanar gizo, inda ake tsare da shi bisa zargin damfara.

Wasu masu zaukar bidiyo biyu da suka ziyarce shi sun tabbatar da kama shi, yayin da wani jami’i daga sashen yaƙi da laifukan yanar gizo ya shaida wa AFP cewa, “yaudara da bokanci” abin hukunci ne a dokar Mali.”

Jami’in ya ce da wahala a ɗauki mataki tun lokacin da gasar ke gudana, domin yanayin zafi da sha’awar da ke tattare da AFCON. “Da wuya a kama shi yayin da gasar ke ci gaba,” inji shi.

By ukarofi