Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kungiyar Dattawa da shugabannin Jihar Ribas, ta nuna damuwa kan sanarwar neman tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Ordu.
Shugaban riƙon ƙungiyar, Dr. Gabriel Toby, wanda tsohon mataimakin gwamnan jihar ne, ya soki wannan yunkuri a cikin wata sanarwa da aka fitar a Fatakwal ranar Asabar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya rawaito cewa ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas sun bayyana shirinsu na tsige Fubara bayan wani taron gaggawa da suka yi ranar Laraba.
Mr Toby ya ja hankalin cewa tsigewa wani muhimmin tsari ne a kundin tsarin mulki, bai kamata a yi amfani da shi don biyan buƙatun siyasa ko rikicin ɓangaranci ba.
A cewarsa, dalilan da ‘yan majalisar suka bayar don yunƙurin tsige gwamnan ba su da ƙarfi, ba su da inganci kuma babu wani uzurin da ya shafi muradun jama’a ko kuma da ya yi daidai da tanadin kundin tsarin mulki.
