Gidauniyar Manar El-Huda ta horas da mata akan kyautata zamantakewar aure

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An bayyana iyaye mata da cewa daga wajensu ne ‘ya’ya suke samun tarbiyya kaso 80 cikin 100  su kuma iyaye maza sune ke bayar da kaso 20 domin haka ake so a samu uwa tagari da za a  samu zuri’a mai cike da kyakkyawar tarbiyya.

Babban shehin malamin addinin Musulunci Farfesa Umar Sani Fagge ne ya bayyana hakan a  cikin jawabinsa a yayin taron yaye mata da aka horar dasu akan tarbiyyar zaman aure a ƙarƙashin Gidauniyar Manar El-Huda da aka gudanar a makarantar firamare ta Fagge a ranar  Asabar.

Malam Umar Sani Fagge ya yi nasiha sosai ga iyaye mata da akan yadda za su mutunta kansu da kula da mazajensu da kuma tarbiyyar ya’yansu da hakan zai jawo musu natsuwa da kulawa a rayuwar zamantakewar aure da alkhairi a duniya da lahira.

Malama Fatima Muhammad Fagge shugabar Gidauniyar Manar El-Huda da take bayini  akan maƙasudin taron ga ‘yan jarida ta ce taron an gudanar da shi ne akan abubuwa biyu na cika addu’a ne na  kammala saukar ƙur’ani da ɗaliban Makarantar Manar El-Huda suka gudanar don roƙawa ƙasa samun zaman lafiya da yiwa  iyaye da mazajensu da ya’yansu  da malamansu da dukkan alummar Annabi a duniya  addu’a akan samun zaman lafiya da yalwar arziƙi da kariya daga dukkan fitintinu.

Ta ce an yi sauka sau 12,000 shine suka gayyato  Shehun malaminsu   Umar Sani Fagge ya zo ya ƙarƙare  yin addu’a. Sannan kuma taron ya haɗa da yaye ɗalibai mata da aka baiwa horo na musamman na zaman gidan aure  da adadin su ya kai guda  680 an bayar da shaida ga matan aure da zawarawa da yan mata da suka sami horon.

Ta ce an soma bada horon ne a shekara ta 1439 da ya yi daidai da shekarar  2018 yanzu sun haɗa adadin yawan ɗalibai da suka sami horo  5,84,00  kuma irin tasirin da horon ya haifar ana samun shaida daga  mazaje sukan kirawo su su shaida musu hatta ya’yan suma kan kira su saboda sun ga kyakkyawan  sauyi a halayyar matan dana iyaye.

Ta ce basu ma fiye sauraren ɗalibai ban  nasu bs sun fi sauraren irin shaidar da mazaje suke gaya musu  domin miji shine zai ga zahiri akan abinda suka bada horo akai wannan basu da abinda za su ce kan nasarori da ake samu sai daɗa godiya ga Allah.Kuma  ana bayar da horonne na  tsawon watanni Uku mako 12 kenan  idan  ba wani abu ne ya ratsa ba an kammala.

Malama Fatima Muhammad Fagge ta ce karramawar da suka yiwa Malaminsu Farfesa Umar Sani Fagge ta matsayinsa na  uba ne, malami, shugaba, mai bada tarbiyya ne mai nusantarwa ne mai kuma hangen nesa kuma ubangidansu ne saboda haka kyauta da suka bashi na karramawa tana ganin sun ma ƙaranta.

Ya ce ita wannan gidauniya ta Manar El-Huda hannunta a bude yake duk inda ta kaya suna shiga ko a yanzu makarantu 146 da suke dasu a cikin Kano wannan ya nuna ba karamin al’amari bane kuma har ƙauyuka suna shiga sai ka tatar da mace a cikin lungun ƙauye da kafin mota ta shiga sai jiki ya jigata amma sun shiga sun ɗora ta akan saiti mazajensu na yi musu godiya har a Kaduna  da Katsina sun baiwa mata horo.

Ta ce ita Gidauniyar Manar El-Huda tana da shiri na koya kwana wanda duk yake ganin sammakon fitowa ba zai masa ba in ya gayyace su za suje har gida su yiwa iyalinsa horo akan inganta zaman aure domin gundarin abinda yake faruwa a zaman aure yanzu sun lura ba shine koyarwar musulunci yazo dashi ba ana buƙatar duk inda za a  asa hannu ayi gudunmuwa a isar da abinda Annabi ya koyar akan aure  za a je ko a ina ne.

Malama Fatima Muhammad  ta ce saboda tsaftace harkokin biki da mata suke yi ita kanta ta shiga ciki ta kan yi DJ. suna yin waƙoƙin da ake taƙama da su a dandalin biki, tuni ma har  sunyi nasarar  mayar dasu wa’azi na gidan aure, da an buga kalangu da waƙe yadda za a yi maka wancan kaji haka za a buga maka wannan da kanka za kaji kalmomin da bambanci domin tuni malam ya ɗora su akan yanda za suyi.

Ta ce  kafin ma aje ga buge-bugen waƙoƙi  sun iya riƙe mata ayi kamun buki da yin  tafi  ayi ana addu’a ana salatin Annabi da karatun ƙur’ani wanda  yanzu ma Kano ta ɗauki wannan tsarin da yawa ana zuwa  ma a  gayyace su don ita kanta daga nan ta je har Kaduna da Abuja ta shiga gidan gwamnati da wurare da dama akan kamun amarya kuma  sun gode Allah  al’amarin yana karɓuwa.

Malama Fatima Muhammad Fagge ta ce bata da wani abu da take ji yake  yi mata daɗi a faɗin duniya irin yanda Allah yake amfani da su a yin hidimar addinin musulunci kuma ƙololuwar burinta shine Allah ya karɓi ayyukan da suke  yi.

By ukarofi