Jirgin Ƙatar Airways ya yi saukar gaggawa da fasinjoji 260 a Legas

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Juma’a ne wani jirgin sama na Kamfanin Qatari Airways da ke ɗauke da fasinjoji 248 da ma’aikata 12 ya yi saukar gaggawa a Filin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas jim-kaɗan bayan tashinsa.

Al’amarin ya faru ne sakamakon lalacewa daga wani sashinsa.

Majiyoyin filin jiragen sama sun shaida wa manema labarai a yau Asabar cewa matuƙin jirgin ya sanar da jami’an kula da hanyoyi (ATCs) matsalar jim-kaɗan da tashinsu, lamarin day a sa ya nemi saukar gaggawa kuma aka amince masa nan take.

Da yake tabbatar faruwar al’amarin, Sakataren yaɗa labaran Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Legas (LASEMA) Dakta Olufemi Oke-Osanyintolu a wata sanarwa, ya ce jirgin ya samu tsaiko ne a ɓangaren gudanarwa sakamakon ɗumamar yanayi na sararin samaniyar Nijeriya, lamarin da ya haddasa al’amarin gaggawar.

Ya ƙara da cewa, baki ɗaya fasinjoji da jami’an jirgin sun fito cikin aminci ba tare da rahoton rauni ko rasa rai ba.

Haka kuma, babu wani babban dameji da hakan ya haifar wa jirgin, kamar yadda hukumar ta bayyana.

By Babaji